Da dumi-dumi: Yan sa’o’i kafin zaben fidda gwani na PDP a Kogi, yan takara 7 sun janyewa Idris Wada

Da dumi-dumi: Yan sa’o’i kafin zaben fidda gwani na PDP a Kogi, yan takara 7 sun janyewa Idris Wada

Rahotanni sun kawo cewa yan takara bakwai da ke neman tikitin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Kogi, sun janyewa tsohon gwamnan jihar, Kyaftin Idris Wada.

Yan takarar wanda suka janye sun fito ne daga yankin gabashin jihar.

Kungiyar dattawan Kogi ta gabas ta sanar da cewar ta samu tabbacin akalla yan takara bakwai da ke shirin jinginar da kudirinsu domin marawa takarar Wada baya.

Mataimakin Shugaban kungiyar, Architect Gabriel Adukwu ya bayyana cewa kungiyar ta nuna damuwa akan yawan yan takarar da suka nuna ra’ayinsu akan kujerar gwamna.

A cewarsa hakan yasa kungiyar ta yi zama da dama tare da yan takarar domin Jan hankalinsu akan su janyema dan takara guda.

Yace bakwai daga cikin yan takarar gwamna 16 na PDP daga yankin Kogi ta gabas sun janyewa Idris Wada.

Wadanda suka janyewa Wada sun hada da Air Vice Marshall Salihu Atawodi mai ritaya, Muhammed Tetes, Emmanuel Omebije, Misis Grace Iye Adejor, Dr Victor Adoji.

Ya bayyana cewa zango guda kawai Wada zai yi.

KU KARANTA KUMA: Lamarin Wadume: Rundunar yan sanda ta sake kama wasu mutum 11

Haka zalika da yake magana, tsohon mataimakin gwamnan tsohuwar jihar Benue, Sule Iyagi ya bayyana cewa sub yanke shawarar janyewa Wada ne saboda tarin saninsa sannan ya kara da cewa hakan me babban dalilin da yasa suka roki sauran yan takarar akan su janye masa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel