Tura Ta Kai Bango: Matakin da Jam'iyyar PDP Ke Shirin Dauka kan Nyesom Wike
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, na ci gaba da zama karfen kafa ga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Jam'iyyar PDP ta shirya daukar matakin ladabtarwa kan Wike wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Rivers
- Shirye-shiryen daukar matakin dai na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke shirin gudanar da babban taronta na kasa a birnin Ibadan na jihar Oyo
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP, na duba yiwuwar daukar matakin ladabtar kan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Kwamitin na NWC na iya yanke shawarar korar Nyesom Wike, daga cikin jam’iyyar PDP.

Source: Facebook
A cewar rahoton Daily Trust, wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar sun ce lokaci ya yi da za a dauki mataki a kan tsohon gwamnan na jihar Rivers.
Sun ce ya kamata a dauki matakin ne saboda yadda yake ci gaba da kawo rikici cikin jam’iyyar.
Meyasa PDP za ta kori Wike?
Wani babban jami’in jam’iyyar da bai so a ambaci sunansa ba, ya bayyana cewa idan kokarin sasancin da kwamitin da shugaban kwamitin amintattu (BoT), Sanata Adolphus Wabara, ke jagoranta ya gaza, za a kori Wike daga jam’iyyar.
“Kamar yadda kake gani, Minista Wike yana son komai ya kasance yadda yake so kawai. An yi kokari da dama daga gwamnoni da abokansa domin ya sauko, amma ya ki sauraro."
"Abin da kaɗai zai iya hana korarsa shi ne idan kwamitin Wabara ya samu nasarar sasanci, wanda ba na ganin hakan zai yiwu. Da zarar hakan ya gaza, za a ɗauki mataki a babban taron jam’iyyar."
“Ba za ka kasance babban jigo a PDP sannan ka fito fili kana tallata dan takarar APC a zaben 2027 kuma ka sa ran cewa babu abin da za a yi maka ba. Wannan ba zai yiwu ba.”

Kara karanta wannan
Rikicin PDP: Shugabananni a jihohi 36 sun raba gardama tsakanin Damagum da tsagin Wike
- Wata majiya
Shawarar korar Wike ta samu karbuwa a NWC
Wani babban jami’in jam’iyyar daga yankin Arewa ma ya tabbatar da cewa mambobin NWC karkashin Umar Damagum sun fara amincewa da shawarar korar Wike, wanda ake ganin ya kamata a dauka tun kafin rikicin PDP ya tsananta.

Source: Facebook
“Yanzu shugabannin jam’iyyar suna ganin gara a ce an makara da a ki daukar mataki. Kora ce kawai mafita, tunda duk kokarin sulhu tun bayan rikicin 2023 ya gaza."
"Ba ma sa ran kwamitin Wabara zai yi wani abin mamaki. Idan suka samu yawan goyon bayan da suke nema, to korar Wike da magoya bayansa ita ce hanyar da ta rage."
- Wani jigon PDP
Wike ya caccaki shugaban PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi kalaman suka kan shugaban jam'iyyar PDP na kasa.
Wike ya bayyana Umar Damagum a matsayin mutum mara ladabi wanda bai cancanci jagorantar jam'iyyar PDP ba.
Ministan ya ce Damagum mutum ne da ke gudanar da harkokinsa bisa son kudi kawai, ba tare da la’akari da amana ko ka’ida ba.
Asali: Legit.ng

