Ziyarar Matawalle zuwa Zamfara Ta Tayar da Kura Tsakanin Jam'iyyun APC da PDP

Ziyarar Matawalle zuwa Zamfara Ta Tayar da Kura Tsakanin Jam'iyyun APC da PDP

  • Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Mohammed Matawalle na shirin kai ziyarar zuwa jiharsa ta Zamfara
  • Jam'iyyar APC ta yi zargin cewa PDP ta damu matuka kan ziyarar da tsohon gwamman yake shirin kai wa jihar
  • Hakazalika, APC ta yi fatan cewa wasu karin jiga-jigai daga jam'iyyar PDP za su ci gaba da sauya sheka zuwa cikinta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta taso abokiyar hamayyarta PDP a gaba kan ziyarar Bello Matawalle.

Jam'iyyar APC ta ce PDP ta nuna rashin jin dadinta da ziyarar da karamin ministan tsaron ke shirin kawowa zuwa jihar.

Ziyarar Matawalle zuwa Zamfara ta tayar da hazo tsakanin PDP da APC
Karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle Hoto: Dr. Bello Mohammed Matawalle
Source: Original

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Malam Yusuf Idris, ya fitar a ranar Litinin a Gusau.

Kara karanta wannan

Damagum: Shugaban PDP ya fadi dalilin kin hukunta masu kawo cikas a jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me APC ta ce kan PDP a Zamfara?

Ya ce martanin PDP kan ziyarar ministan ya nuna cewa jam’iyyar mai mulki ta damu matuka kuma ta shiga rudani.

"Jam’iyyar PDP mai mulki a Zamfara ta rikice, ta watse kuma tana cikin tsoro. A kowane lokaci, mambobinta ciki har da manyan mutane da magoya baya suna barin jam’iyyar saboda gazawarta."

- Malam Yusuf Idris

Yusuf Idris ya yi watsi da wani bayani da aka danganta kan mai magana da yawun PDP na jihar, Halliru Andi, wanda ya ce ya kamata Matawalle ya soke ziyarar tasa ya zauna a ofishinsa a Abuja.

Ya bayyana cewa ministan, kasancewarsa jami’in gwamnatin tarayya, yana da cikakken hakkin ziyartar kowane sassa na Najeriya, ciki har da jiharsa ta haihuwa.

Yusuf Idris ya kara da cewa a baya Matawalle ya gudanar da ayyukansa daga jihar Sokoto bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, lokacin da, a cewarsa, Gwamna Dauda Lawal ya hana shi gudanar da ayyukansa daga Zamfara.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa Gwamna Diri bayan komawa jam'iyyar APC

Ya ce wannan ziyarar da ministan ke shirin yi ta haifar da tsoro a cikin PDP, amma ya jaddada cewa zai kawo ziyarar saboda amincewar fadar shugaban ƙasa.

“A matsayinsa na ɗan asalin Zamfara kuma jagoran APC a jihar, yana da cikakken hakkin ziyartar mutanensa, jam’iyyarsa da magoya bayansa."

- Malam Yusuf Idris

Ya kuma soki PDP saboda yin suka a baya kan ziyarar da ‘yan Zamfara ke kai wa Matawalle a Abuja, yana mai cewa jam’iyyar na kokarin tsoma baki cikin harkokin ministan.

Mai magana da yawun na APC ya bayyana cewa jam’iyyar na maraba da ministan, tare da fatan cewa karin ‘yan siyasa, musamman daga PDP za su koma APC.

APC ta ragargaji PDP kan Matawalle
Bello Matawalle mai rike da mukamin karamin ministan tsaro a Najeriya Hoto: Dr. Bello Mohammed Matawalle
Source: Original

APC ta kalubalanci PDP

Yusuf Idris ya kuma kalubalanci PDP da ta maida hankali kan gudanar da mulki, yana mai kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Ya zargi gwamnan da yawan zama a kasashe. waje a lokutan da ake bukatar jagoranci, yana nuni da hare-haren da aka kai kwanan nan inda aka kashe mutane ko aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

'Yan NNPP sun bar kwankwasiyya, mutum 1000 sun koma APC a Kano

Ya yi zargin cewa gwamnan ya tafi kasashen waje domin bikin kammala karatun ɗansa a lokacin da al’ummomi da dama a Zamfara ke fama da hare-hare.

Har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, PDP reshen Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa kan zarge-zargen da APC ta yi ba.

APC za ta kai PDP kara kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta nuna rashin jin dadinta kan wasu kalaman da PDP ta yi kan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Jam'iyyar APC ta yi barazanar daukar matakin shari'a kan PDP bisa zargin da ta yi wa Matawalle kan hannu a matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar.

Hakazalika, jam’iyyar APC ta bayyana zargin a matsayin ƙarya, ɓatanci, wanda yake cike da siyasa a cikinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng