INEC na Fuskantar Matsin Lamba kan Zaben Anambra, Hukumar Ya Yi Magana kan BVAS
- Hukumar INEC ta tabbatar da cewa ta kammala duk shirinta na gudanar da sahihin zaben gwamnan jihar Anambra yau Asabar
- INEC ta ce ba za a samu wata tangarda da na'urar BVAS ko jinkirin kayan zabe ba, kuma ma'aikata za su isa wurin aikin da wuri
- Hukumar ta tabbatar da cewa ta shirya gudanar da zabe zagaye na biyu idan har babu 'dan takarar da ya cika sharuddan doka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra — Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi karin haske game da zaben gwamnan Anambra da za a gudanar yau Asabar.
INEC ta tabbatar da da cewa ta kammala dukkan shirye-shiryenta don gudanar da sahihin zaben jihar da kowa zai gamsu da shi a yau, 8 ga Nuwamba, 2025.

Source: UGC
INEC ta yi karin haske kan zaben Anambra
Wani kwamishinan INEC na kasa, Ken Ukeagu, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da Channels TV a a daren Juma'a, 7 ga Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ken Ukeagu, ya jaddada cewa an tura dukkan kayan zabe da ma’aikata, sannan an riga an cimma tsare-tsare na yin zaben cikin nasara.
“Aikin mu shi ne mu gudanar da zabe na gaskiya da adalci ga al’ummar Anambra da Najeriya baki ɗaya, kuma za mu tabbatar da hakan a gobe (Asabar).”
- Ken Ukeagu, Kwamishinan INEC.
INEC ta magantu kan amfani da BVAS
Hukumar INEC dai ta fuskanci matsin lamba daga ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki don tabbatar da gudanar da zabe mai tsafta a Anambra,
An yi matsin lambar ne bayan matsalolin da aka fuskanta a wasu zabubbuka da suka gabata, kamar jinkirin isar kayan zabe, matsalar BVAS, da jinkiri wajen kai ma’aikata.
Sai dai Ukeagu ya tabbatar wa al’umma cewa INEC ta gyara duk wadannan matsaloli, tare da tabbatar da cewa ma’aikata da kayan zabe za su isa wuraren kada kuri’a da wuri.
“Ba za mu samu wata matsala ba. Ba za a samu tangardar nau'urar BVAS ba. Kayan zabe da ma’aikata za su isa da wuri, kuma zaben Anambra zai kasance sahihi."
— Ken Ukeagu.

Source: UGC
INEC ta shirya wa matsalolin da za su biyo baya
A yayin da yake karin bayani, Ukeagu ya tabbatar da cewa INEC ta tanadi shirye-shirye na musamman idan ba wanda ya cika ka’idojin lashe zaben gwamna a zagayen farko.
Ukeagu ta ce:
“Mun shirya idan za a sake zabe. Ka san, doka ta tanadi hakan – idan babu wanda ya cika sharuddan doka, za mu gudanar da zagaye na biyu."
Kwamishinan ya nanata cewa INEC za ta kasance mai zaman kanta kuma ba za ta nuna son rai ba, tare da tabbatar da cewa za a kirga kuri’un al’umma yadda ya dace.
'Yan Najeriya sun hango wanda zai ci zaben Anambra
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'Yan takara 16 ne za su fafata a zaben gwamnan Anambra na yau Asabar, ciki har da Gwamna Charles Soludo.
Kashi 53.5 na wadanda suka kada zaben ra'ayi da Legit.ng ta gudanar a soshiyal midiya sun nuna Soludo ne zai ci zaben.
Masana siyasa sun ce karfin mulki da tasirin jam’iyyar APGA na iya tabbatar da tazarcen Gwamna Charles Soludo a zaben ranar Asabar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


