Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja

Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja

  • Hukumar INEC ta shirya gwajin tantancewa na kafin zabe a Abuja, Legas da Imo da na’urar BVAS a rumfunan zabe 436 daga cikin 176,846
  • A jihar Legas, jama’a sun fito kwansu da kwarkwata kuma sun tabbatar da cewa na’urar BVAS tayi aiki yadda ya dace
  • Wadanda suka halarci tantancewar sun yabawa INEC tare da cewa hukumar ta shirya tsaf domin zaben 2023 din mai zuwa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC a ranar Asabar ta yi gwajin tantance masu kada kuri’u da na’urar BVAS.

Mahmoud Yakubu, shugaban hukumar, ya sanar da cewa za a yi gwajinw a rumfunan zabe 436 daga cikin 176,846 da ke fadin kasar nan kafin zuwan zabe.

Hotunan Farfesa Mahmoud Yakubu
Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja. Hotuna daga vanguardngr.news
Asali: UGC

Legas

Yayin da TheCable ta ziyarci karamar hukumar Ikeja ta jihar Legas, rahotanni sun nuna ana gwajin lafiya kalau a rumfunan zaben.

Kara karanta wannan

Assha: Dan takarar majalisa a jam'iyyar su Kwankwaso a Arewa ya sace N681m daga asusun banki

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jami’an hukumar sun isa rumfunan zabe wurin karfe 8 na safe a titin Irewole/Joseph. Da karfe 9:30 na safe, sama da masu kada kuri’a 15 aka tantance daga cikin 500 da ke da rijista a rumfar zaben.

Yayin zantawa da TheCable, Gabriel Taire, jami’in INEC da ke rumfar yace ya gamsu da yawan jama’a da suka fito.

Yace sakamakon tantancewar gwajin ta nuna cewa INEC ta shirya tsaf don zaben.

“Gwajin zaben ya matukar birgewa kuma gwanin sha’awa. A yanzu, mun tantance kusan mutum 13 kuma babu wanda bai tantantu ba.”

- Yace.

“Na gamsu da yawan mutanen da suka fito. A wasu gundumomi inda aka yi gwajin, ba a samu matsaloli ba. An yi shi lafiya kalau. Mun tsammaci hakan yayin zabe.”

A Anifowose/Ikeja PU, masu kada kuri’a 23 aka tantance cikin 543 masu rijista a rumfar zaben.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Kuma Sukar Mulkin Shugaba Buhari a Gaban Jama’a Wajen Yawon Kamfe

Madam Chinyere, daya daga cikin wadanda aka tantance ta yabawa INEC kan cigaban da aka samu inda tace BVAS za ta saukaka zabe.

“INEC ta nuna cewa ta shiryawa zaben 2023 kuma muna yabawa kokarinta.”

- Tace.

Jami’an tsaro sun yawaita da dukkan rumfunan zaben da aka yi gwajin tantancewar.

Abinda ya faru a Abuja

A Abuja kuwa, duk da BVAS tayi aiki babu matsala, mazauna yankunan kadan ne suka fito domin gwajin tantancewar.

A rumfar zaben da ke Area 10, jama’a da yawa ba su fito ba yayin da aka tantance mutum 10 kacal a yankin Karu.

Jama’ar Imo sun yi tururuwar fitowa

Mazauna yankin da rumfar zabe ta Iho da ke karamar hukumar Ikeduru a jihar Imo sun fito kwansu da kwarkwatarsu.

Nobleiyke Edoziem, wani shugaban yankin wanda ya zanta da TheCable yace tabbas lamarin akwai inganci.

“Idan kayayyakin da za a yi amfani da su a zaben ranar 25 ga wata za su dinga aiki da kyau kamar na gwajin nan, ina tabbatar da cewa za a samu sakamako mai kyau zuwa karshen ranar.”

Kara karanta wannan

Zamu Tabbatar Da Kun Samu Isasshen Mai Lokacin Zabe: NNPC Ya T

- Edoziem yace.

Christopher Ogudiri, wani mazaunin yankin, ya tabbatar da cewa mutane da yawa za su fito don gwajin.

Ga hotuna:

Gwaji
Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja. Hoto daga. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Gwaji
Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Gwaji
Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Gwaji
Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Gwaji
Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Gwaji
Hotunan Yadda Ake Gwajin Tantancewa da Na’urar BVAS a Jihohin Legas, Imo da Abuja. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Wasiyyar da Sarkin Dutse ga Bola Tinubu a ziyarar da ya kai masa ta narka zukata

A wani labari na saban, Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar shugaban kasa na APC tare da rakiyar gwamnoni 6 da wasu manyan ‘yan siyasa sun gana da marigayi Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi a mako biyu da suka wuce.

Basaraken ya yi kira ga Tinubu da ya shawo kan matsalar rashin ruwa da ya addabi babban birnin jihar Jigawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel