Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamnan Anambra Ke Gudana, APGA, APC da LP Sun Ja Daga

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
10 Posts
Sort by
Our live updates have concluded for the day. Catch up on everything you missed below.
Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Ana sayen kuri’u a zaben gwamnan Anambra

Ana zargin cewa a karamar hukumar Onitsha ta Arewa, ana neman wadanda za su aida kuri’unsu domin samun kudi.

A wata rumfa da ke garin na Onitsha, an rahoto cewa wakilan jam’iyyu na kokarin sayen ra’ayin jama’a a kan N20, 000.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

An yi wa mai sa ido barazana

Wani mai sa ido daga Centre for Journalism Innovation and Development (CJID) ya fuskanci barazana da cin zarafi, a unguwar Mary de Queen, Uzoakwa inda ake da rumfunan zabe na 017 da 015.

A wajen, an kwace masa wayar hannu yayin da yake zargin ana sayar da kuri’a a yankin.

An tabbatar cewa mai sa idon yanzu yana cikin koshin lafiya, an kuma mayar masa da wayarsa, kuma yana St. Anthony, Umuoye, Okija.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Gwamna Soludo ya kada kuri'a

Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, tare da matarsa Nonye Soludo, sun kada kuri’unsu da misalin karfe 1:20 na rana a ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, a rumfar zaɓensu da ke Isuofia.

Da yake magana da manema labarai bayan kada kuri’a, gwamnan ya zargi wani ɗan takarar wata jam’iyya da yin sayen kuri’a. Ya yi zargin cewa ana kokarin rinjayar masu zaɓe a rumfar zaɓensa.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Dan takarar ADC ya kada kuri'a

Dan takarar jam’iyyar ADC a zaben gwamnan jihar Anambra, John Nwosu, ya kada kuri’arsa.

John Nwosu ya kada kuri'arsa ne a Oduda Central School, Ward 2, da ke karamar hukumar Nnewi ta Arewa.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Dan takarar LP ya kada kuri'a

Dan takarar jam’iyyar LP, George Moghalu, ya kada kuri’arsa.

George Moghalu ya kada kuri'arsa ne a rumfar zaɓe ta 017, Uruagu Ward 1, da ke karamar hukumar Nnewi ta Arewa.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Yan kasuwa sun fifita kasuwanci kan zaɓe

Duk da zaben gwamna da ake yi a Jihar Anambra, harkokin kasuwanci sun ci gaba kamar yadda aka saba a kasuwar Nkwo Awkuzu a ranar Asabar, inda ‘yan kasuwa da mazauna yankin suka ci gaba da aikinsu na yau da kullum. Titunan da ke cunkushe da jama’a sun kasance cike da motocin hawa, yayin da shagunan sayar da kayan abinci, kayayyakin masarufi da sauran kaya suka kasance a bude. Daily Trust ta ce ‘yan kasuwa sun shaida wa ‘yan jarida na CJID cewa sun fi son gudanar da kasuwanci maimakon fita kada kuri’a.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Makaho ya zabi gwamna a Anambra

Vanguard ta rahoto cewa wani makaho mai suna Pa Julius Nwafor ya kada kuri’arsa a unguwar Isuofia da ke karamar hukumar Aguata.

Diyarsa mai suna Ofeoma Nwafor ta taimakawa dattijon mai shekara 74 ya yi zabe.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Wakilin jam'iyya na ba masu kada kuri'a takardu

Jaridar The Cable ta ce a rumfar zabe ta 003 a mazaba ta 8 da ke Nnobi a karamar hukumar Ndemili, an hango wani wakilin jam'iyya na raba takardu ga masu kada kuri'a.

Waikilin jam'iyyar yana mika musu takardar ne bayan sun kada kuri'unsu. Hakazalika yana rubuta sunayensu a cikin wata takarda.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Halin da ake ciki a mazabar Peter Obi

Bayanai daga Legit sun bayyana halin da ake ciki a rumfar zaben Peter Obi, babban jagoran hamayya a Najeriya.

Peter Obi yana kada kuri'arsa ne a akwati ta 19 da ke rumfa ta 2 a yankin Agulu a karamar hukumar Anaocha a Anambra.

Kafin karfe 10:00 na safe aka ga wasu jami'an tsaro biyu sun hallara a rumfar zaben bayan hayaniya da aka nemi a samu.

Muhammad Malumfashi avatar Sharif Lawal avatar Abdullahi Abubakar avatar
daga Muhammad Malumfashi, Sharif Lawal and Abdullahi Abubakar

Jami'an INEC sun fara tafiya rumfunan zabe

Jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) sun fara tafiya zuwa rumfunan zaɓensu a karamar hukumar Awka ta Kudu.

Tashar Channels tv ta ce ma’aikatan wucin gadi na INEC sun isa makarantar firamare ta Amawbia, wadda ke kula da mazabu 01 da 02 a cikin karamar hukumar Awka ta Kudu, da misalin karfe 7:07 na safe.

An kuma ga motoci masu ɗauke da kayan zaɓe suna barin wurin yayin da jami’an hukumar suka fara tafiya zuwa wuraren da aka raba su domin gudanar da aikin zabe