Tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau Ya Yi Magana kan Lokacin da Zai Daina Siyasa

Tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau Ya Yi Magana kan Lokacin da Zai Daina Siyasa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya tabo batun daina shiga cikin harkokin siyasa
  • Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ya dauki siyasa a matsayin abu mai muhimmanci wanda ba zai iya dainawa ba
  • Tsohon ministan ya bayyana cewa tun da farko ya gina siyasarsa ne a kan tafarkin addini da dabi'a, kuma yin takara a zabe ba bakon abu ba ne a wajensa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi tsokaci kan lokacin da zai daina yin siyasa.

Ibrahim Shekarau ya sha alwashin cewa zai ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa har karshen rayuwarsa.

Shekarau ya ce ba zai daina siyasa ba
Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau Hoto: Ibrahim Shekarau
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Kano, a wani bangare na bukukuwan cikarsa shekaru 70 da haihuwa a duniya.

Kara karanta wannan

Tsohon darektan DSS ya tsoratar da Najeriya a kan barazanar Trump, ya bada mafita

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekarau ya yi magana kan siyasarsa

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya gina siyasarsa ne bisa tafarkin addini da dabi'a.

“Siyasata addinina ce, addinina kuma siyasata ce.”

- Sanata Ibrahim Shekarau

Ya kara da cewa ba zai daina siyasa ba, domin shiga cikin tsarin samar da shugabanni nagari wani bangare ne na hidima ga jama'a, kuma wajibi ne a cikin addinin Musulunci.

“Ba zan bar siyasa ba saboda shiga cikin tsarin samar da shugabanni masu gaskiya da amana ibada ce a Musulunci."

- Sanata Ibrahim Shekarau

Shekarau ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne ba don neman mulki ko jin dadi ba, sai don ya taimaka wajen ganin ana samar da shugabanni adalai da kwararru masu hidimtawa jama’a bisa gaskiya.

“Matukar ina da karfi da damar bada gudunmawa a kowace hanya, zan ci gaba da yi. Siyasa a gare ni ba aiki ba ne da yake karewa ba, nauyi ne na rayuwa gabadaya."

Kara karanta wannan

Musulmi, Zohra Mamdani ya lashe zaben Amurka duk da barazanar Trump

- Sanata Ibrahim Shekarau

Wace nadama Shekarau ya yi a siyasa?

Tsohon ministan ya ce bai taɓa nadama kan tafiyar siyasarsa ba duk da kalubale da gazawar da ya fuskanta, domin kullum yana karɓar abin da ya same shi a matsayin nufin Allah.

Shekarau ya tabo batun daina siyasa
Malam Ibrahim Shekarau wanda ya taba zama gwamnan Kano Hoto: Ibrahim Shekarau
Source: Facebook
“Duk abin da ya same ni, na ɗauke shi a matsayin hukuncin Allah. Ko da na kasa cimma abin da nake fata, ina daukar hakan a matsayin Allah Ya zabar min abin da ya fi dacewa da ni. Nadama tana zuwa ne kawai idan mutum bai yarda da hukuncin Allah ba.”
Da yake waiwayar farkon siyasarsa, Shekarau ya ce tun a lokacin da yake dalibi a shekarun 1980 yake shiga zaɓe, inda ya rike mukamai daban-daban a kungiyoyin malamai da cibiyoyin ilimi.
“Don haka zaɓe ba sabo ba ne a gare ni. Tun 1982 nake shiga zaɓe, kuma zuwa 1988, na zama makarantun ’yan sanda na kasa a Najeriya, ina kula da makarantu sama da 8,000."

Kara karanta wannan

Zargin kisan kiristoci: Wike ya zargi 'yan adawa da wuce gona da iri wurin yada karya

- Sanata Ibrahim Shekarau

Shekarau ya yi magana kan kifar da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan shirin kifar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa hadakar kawai da za ta iya kayar da Shugaba Tinubu a shekarar 2027, ita ce wadda jam’iyyu suka hadu kai tsaye, ba daidaikun mutane ba.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa daidaikun mutane da ke neman mulki ba za su iya kifar da Tinubu ba a zaben 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng