An Taso Abba Kabir a gaba, APC Ta Fadi yadda Za Ta Kwace Mulkin Kano Karfi da Yaji
- Shugaban jam'iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas, ya kuma yin bayani dalla-dalla na yadda za su kwace mulkin jihar a zaben 2027
- Abbas ya ce jam’iyyar su za ta hana Gwamna Abba Kabir Yusuf komawa kan mulkin Kano a 2027, koda me zai biyo baya
- Ya kuma soki rikicin masarautar Kano, yana kiran samar da sarakuna biyu da “lalata tarihi” da cewa gwamnatin Abba ta lalata masarauta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana yadda za su kwace mulkin jihar a zaben 2027.
Abbas ya bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa don ganin Gwamna Abba Kabir bai koma mulki ba a Mayun 2027.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Ayuba Salisu Al Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar 2 ga watan Nuwambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta bugi kirji kan zaben 2027 a Kano
A bidiyon, an ga Abdullahi Abbas yana jawabi ga matasan jam’iyya a Gwale, yana cewa Abba ba zai koma kujerarsa ba ko da me zai faru.
Abbas ya ce koda Kano ta zauna lafiya ko ta shiga rudani, ba ya damunsa, domin lallai sai an kawo mulkin wa’adin Gwamna Abba a jihar.
Ya kuma zargi gwamnatin NNPP da rashin kwarewa da cin hanci, yana cewa tun da suka hau mulki, babu komai sai sakaci da wawashe dukiya.
Ya ce:
"Duk abin da zai faru a Kano sai dai ya faru, sai mun fitar da Abba Kabir a mulki, ba ma ji ba ma gani duk abin da za a yi a Kano sai dai a yi.
"Ko a zauna lafiya ko ka da a zauna, ku yan soshiyar midiya to sai ku shirya, idan mutum ya san yana tsoro, ya je ya zauna a gida kawai."

Source: Facebook
APC ta yi magana kan rikicin masarauta
Game da rikicin masarautar Kano, Abbas ya bayyana cewa kafa sarakuna biyu abin kunya ne, yana cewa wannan lamari ya bata tarihin birnin Kano sosai.
Abbas ya kuma taba Rabiu Musa Kwankwaso da yake cewa za su dauki doka a hannu idan aka yi kokarin tada rigima a zaben 2027.
Shugaban APC ya ce su ba sai an kai ga zaben 2027 ba, tun yanzu za su fara kai ruwa rana da duk wani wanda ke rena musu wayo a Kano ko mai girmansa.
Abbas ya yi kaurin sun wurin yin kalamai masu zafi, ya kasance cikin masu suka sosai tun bayan da NNPP ta karɓi mulki daga APC a shekarar 2023.
'Yan Kwankwasiyya 1000 sun koma APC
Mun ba ku labarin cewa wasu yan jam’iyyar NNPP sama da 1,000 sun sauya sheƙa daga jam'iyya mai mulki a Kano saboda wasu dalilai.
Wadanda suka sauya shekan sun yaba da ayyukan da Shugaba Bola Tinubu ke bazawa a Najeriya da jihar Kano.
Sun kuma sanar da cewa daga yanzu sun karbi shahadar APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


