Charles Soludo da 'Yan Takara 3 da za Su Gwabza a Zaben Gwamnan Anambra
A ranar Asabar, Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra zai fuskanci Nicholas Ukachukwu na jam’iyyar APC da wasu ‘yan takara 14 da ke neman kujerarsa a zaben gwamnan jihar Anambra.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Anambra –Daga cikin ‘yan takara 16 da za su fafata a zaben da za a gudanar a ranar 8 ga Nuwamba, 2025, mutum hudu ne kacal ake ganin za su iya kai labari a zaben.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa waɗannan manyan ‘yan takarar su ne: gwamna mai ci, Charles Soludo na APGA; fitaccen ɗan kasuwa, Nicholas Ukachukwu na APC.
Sai kuma tsohon babban darektan Hukumar Ruwa ta Ƙasa (NIWA), George Moghalu na LP da kuma ɗan kasuwa kuma masanin tattalin arziki, John Chuma-Nwosu na ADC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Charles Chukwuma Soludo
This Day ta ruwaito cewa Charles Chukwuma Soludo shi ne gwamna mai ci na jihar Anambra, wanda hakan ke ba shi wani babban rinjaye a kan sauran ‘yan takara.
Soludo na takara a ƙarƙashin APGA, jam’iyyar da ta riƙe mulki a jihar sama da shekaru 20. Yana takara tare da Dr. Onyeka Ibezim, ƙanin Bishof na cocin Anglican, Awka Diocese.

Source: Facebook
Idan aka yi la’akari da tsarin addini a siyasar Anambra, Soludo da mataimakinsa suna da damar nasara saboda Soludo ɗan cocin Katolika ne — addinin da yawanci ke samar da gwamna a jihar.
Ana ganin Soludo da jam’iyyarsa APGA suna da babban damar lashe zaben, musamman ganin yadda jama’a da dama ke ganin ya yi aiki mai kyau a zangonsa na farko.
2. Nicholas Ukachukwu
Nicholas Ukachukwu ɗan kasuwa ne kuma gogaggen mai narka kudi a harkar kasuwancin gidaje, kuma shi ne ɗan takarar jam’iyyar APC.
Ana ganin yana da kyakkyawar damar nasara saboda jam’iyyarsa ce ke mulki a ƙasar nan.

Source: Facebook
Yana takara a tikiti guda tare da Sanata Uche Ekwunife, wadda ta shahara a siyasar ƙasa da ta taba neman kujerar gwamna a baya.
Shahararta na iya ƙara farin jinin Ukachukwu a wannan zabe. Sai dai ƙarancin karatun dan takarar ya zamar masa matsala a yayin kamfen.
3. George Moghalu
Cif George Moghalu, tsohon babban darektan Hukumar Ruwa ta Ƙasa (NIWA), shi ne ɗan takarar jam’iyyar LP a zaɓen jihar.
Ɗan asalin garin Nnewi ne, kuma ya yi ƙoƙari sosai wajen samun tikitin jam’iyyarsa saboda rikicin shugabanci da ke damun jam’iyyar a matakin ƙasa.

Source: Twitter
Moghalu gogaggen ɗan takarar gwamna ne tun zamanin jam’iyyar APP. Yana da goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Peter Obi, amma hakan kadai bai wadatar masa ba don lashe zabe.
Shi ɗan cocin Anglican ne, kuma ana ganin kamfen ɗinsa ya fi karkata wajen sukar gwamnatin Soludo da nuna kura-kuransa, fiye da bayyana shirin kansa ga jihar.
4. Jude Ezenwafor
Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Anambra na ranar 8 ga Nuwamba, 2025, shi ne Cif Jude Ezenwafor.
Ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro, ilimi, hanyoyi da harkar kasuwanci idan aka zaɓe shi.
Ya kuma ce zai rage nauyin haraji da aka dora wa ‘yan jihar domin ƙarfafa harkar kasuwanci da bunƙasa tattalin arziki.

Source: Facebook
Daily Post ta ruwaito cewa a watan Yuli na shekarar 2025 ne aka samu rahoton cewa wasu 'yan sun tare dan takarar tare da bude masa wuta a hayarsa ta komawa gida a babban birnin tarayaa, Abuja.
Makusantansa da wasu daga cikin manyan PDP sun bayyana damuwa cewa wannan lamarin na iya shafar tsarin yakin neman zaben jam’iyyar, musamman idan raunin da Ezenwafor ya tsananta.
Wata majiya ta bayyana cewa:
“Za mu duba yadda lafiyarsa take kafin mu yanke shawara kan yadda za mu ci gaba da kamfen. Muna fatan zai samu sauƙi cikin gaggawa.”
Sai dai Jude Ezenwafor ya murmure, kuma shi da jam'iyyarsa ta PDP sun shirya shiga domin a fafata a zaben ranar Asabar mai zuwa.
An jibge jami'an tsaro a Anambra
A baya, mun wallafa cewa rundunar 'yan sanda ta tura jami’an tsaro sama da 60 000 daga hukumomin tsaro daban-daban domin tabbatar da tsaro a lokacin zaben gwamnan Anambra.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Abayomi Shogunle, ya bayyana cewa an kafa cibiyar ta musamman wacce za ta raba bayanai tsakanin hukumomin tsaro cikin gaggawa domin inganta aiki.
Shogunle ya ce an shirya rundunoni na tsaro a kowace daga cikin rumfunan zabe guda 5,720 a aka samar a fadin jihar domin daukar matakan kare masu kada kuri'a daga duk wani hari ko rikici.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



