Jira Ya Kare: Hukumar NSIEC Ta Fitar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomin Neja

Jira Ya Kare: Hukumar NSIEC Ta Fitar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomin Neja

  • Hukumar zaben Neja (NSIEC) ta ce APC ta lashe duka kujerun ciyamomi a kananan hukumomi 25 da ke jihar a zaben da aka yi ranar Asabar
  • APC mai mulki ta kuma samu nasaran lashe kujerun kansiloli 271 daga cikin 274 yayin da PDP ta ci kujeru biyu kacal
  • NSIEC ta taya daukacin zababbun shugabannin murna tare da fatan za su gudanar da mulki bisa adalci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 25 da ke Jihar Neja.

Kara karanta wannan

Zaben Neja ya bar baya da kura, matasa sun huce fushinsu kan Gwamna Bago

A ranar Asabar da ta gabata, 1 ga watan Nuwamba, 2025 aka gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a fadin jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya.

Jami'an zaben Neja.
Jami'an hukumar NSIEC lokacin da suke aiki a zaben kananan hukumomin jihar Neja Hoto: Abubakar Musa
Source: Facebook

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja (NSIEC) ce ta tabbatar da nasarar APC a sakamakon da ta fitar a Minna, kamar yadda Channels tv ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NSIEC ta ce an yi zabe na adalci

Hukumar ta bayyana zaɓen a matsayin “ingantacce, wanda aka gudanar cikin gaskiya da adalci kuma ya nuna sahihin ra’ayin jama’a.”

A wata sanarwa da Kwamishinan Ayyuka na NSIEC, Mohammed Liman, ya sanya wa hannu, ya ce an kammala tattarawa da sanar da sakamako bisa tanadin dokar zaɓe.

"Bayan nazari, hukumar NSIEC ta amince da sakamakon zaɓen, ta kuma tabbatar da sahihancin zaben ciyamomi da kansiloli da suka cika dukkan sharuddan doka,” in ji Liman.

Wasu daga cikin sababbin ciyamomin Neja

A jerin sunayen da hukumar ta fitar, ‘yan takarar APC ne suka yi nasara a duka ƙananan hukumomi 25, ciki har da Agaie, Bida, Kontagora, Lapai, Bosso, Chanchaga, Wushishi da sauransu.

Daga cikin sababbin shugabannin da aka zaɓa akwai:

Kara karanta wannan

Kama dalibin jami'ar da ya soki gwamna a Facebook ya fara tayar da kura a jihar Neja

1. Sayuti Ibrahim Halilu (Agaie)

2. Usman Mohammed (Bida)

3. Mustapha Jibrin (Chanchaga)

4. Lawal Yusuf (Kontagora)

5. Mohammed Lokogoma (Wushishi)

Yadda APC ta ba 'yan adawa tazara

Sakamakon zaben ya nuna babbar ratar da ke tsakanin APC da jam’iyyun hamayya a yawancin ƙananan hukumomi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Alal misali, a Bosso, APC ta samu 29,140 kuri’u, yayin da PDP ta samu 6,039. A Gbako, APC ta samu 32,310, PDP kuma 7,363; a Suleja, APC ta samu 61,877 yayin da SDP ta samu 1,146.

A Lapai, APC ta samu 43,604, SDP 2,639, PDP kuma 1,429. A Bida, APC ta samu 40,868, PDP 8,386, yayin da a Chanchaga, APC ta samu 25,340, PDP 10,216, SDP 1,137, LP kuma 313, da sauransu.

Gwamna Bago.
Hoton mai girma gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Hoto: @HonBago
Source: Facebook

PDP ta ci kujerun kasila 2 a Neja

Game da kujerun kansiloli kuwa, NSIEC ta tabbatar da sakamakon da jami’ai na mazabu suka bayyana, inda APC ta lashe kujeru 271 daga cikin 274, yayin da PDP ta lashe guda biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kusan N5bn don wasu muhimman ayyuka

Liman ya taya sababbin shugabanni murna, tare da kira gare su da su kasance masu gaskiya, adalci da kishin jama’a yayin gudanar da ayyukansu.

Yan Arewa za su sake zabar Tinubu?

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umar Bago, ya bayyana cewa Arewa za ta ba da cikakken goyon baya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Ya ce yana da yakinin za a yi haka ne saboda Bola Tinubu ya cika dukkanin alkawuran da ya dauka kafin hawa mulki a 2023.

A cewar gwamnan, 'yan Najeriya za su yi mamakin irin kuri'ar da Arewa za ta bai wa Tinubu domin ya yi tazarce zuwa zango na biyu a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262