Daga Shiga APC, Gwamna Diri Ya Yi Wa Tinubu Alkawarin Kaso 99 na Kuri'u a Zaben 2027

Daga Shiga APC, Gwamna Diri Ya Yi Wa Tinubu Alkawarin Kaso 99 na Kuri'u a Zaben 2027

  • Gwamna Douye Diri ya yi alkawarin tara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kusan gaba daya kuri'un jihar Bayelsa a zaben 2027
  • Diri ya dauki alkawarin ne a wurin taron da aka shirya domin tarbarsa bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya karbi Gwama Diri a taron da aka shirya yau Litinin a Yenagoa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa - Gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu alkawarin samun kashi 99 cikin 100 na ƙuri’un jiharsa a zaben 2027.

Gwamna Diri ya bayyana hakan ne a Yenagoa ranar Litinin, yayin bikin tarbar sa zuwa cikin jam’iyyar APC bayan ya fita daga PDP.

Gwamna Douye Diri
Hoton Gwamna Douye Diri tare da kusoshin APC a Bayelsa Hoto: Rabiu Garba Gaya
Source: Facebook

Channles tv ta tattaro cewa taron ya samu halartar manyan kusoshi, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamma Diri ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da kuma wasu gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyar APC sun halarci taron a Yenagoa.

Daga cikin gwamnoni da suka halarci taron akwai Dapo Abiodun (Ogun), Lucky Aiyedatiwa (Ondo), Sheriff Oborevwori (Delta), Hope Uzodimma (Imo), da Umo Eno (Akwa Ibom) da sauransu.

Gwamna Diri ya yiwa Tinubu alkawari

Gwamna Diri ya fice daga PDP a ranar 15 ga Oktoba, 2025, bayan ya nemi shawarwari daga ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki.

Yayin da yake jawabi, Douye Diri ya ce:

“Ni ba mutum ne mai mulki da izza ba. Na zo ne domin mu haɗa kanmu mu yi aiki tare, mu tabbatar da APC ta samu kuri'u kaso 99 cikin 100 a Bayelsa a 2027.

Ya kuma tuna irin soyayya da goyon bayan da jam’iyyar APC ta nuna masa tun lokacin da ya bayyana aniyarsa ta sauya sheƙa daga PDP.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karbi 'yan majalisa 3 da wasu manyan jiga jigai da suka koma APC a Kaduna

Gwamna Diri ya yaba wa yan APC

Douye Diri ya ce dalilin da ya sa ya bar PDP shi ne ganin salon jagorancin gwamnatin tarayya karkashin APC da ke nuna ƙauna da kulawa ga al’ummar Ijaw.

A cewarsa:

“Gwamnatin tarayya ta nuna mana hanya da manufar cewa tana ƙaunar mutanen Ijaw da jihar Bayelsa gaba ɗaya. Kada wani ya yaudare ku, duk wanda yake fadin akasin haka to dan son zuciya ne."
"Tun da na sanar da shirin shiga jam’iyyar APC, dukkanin ’ya’yan jam’iyyar a Bayelsa sun rungume ni hannu biyu-biyu. Don haka ina godiya ga APC da ta karɓe ni da ƙauna.”
Gwamna Douye Diri.
Gwamna Douy e Diri a gidan gwamnatin Bayelsa da ke Yenagoa Hoto: Douye Diri
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa burinsa shi ne haɗa kan ’ya’yan jam’iyyar APC a jihar domin aiki tare da gwamnatin tarayya wajen kawo cigaba ga mutanen Bayelsa, in ji rahoton Vanguard.

Shettima ya karbi Gwamna Diri zuwa APC

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya tarbi Gwamna Douye Diri wanda ya sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta dare gida 2, an dakatar da shugaban jam'iyya na kasa da kan shi

Gwamna Diri, wanda ya bar jam'iyyar PDP a watan Oktoba da ya gabata, ya shiga jam'iyyar APC a hukumance ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025.

Dubban magoya bayan APC da na Gwamna Diri daga lungu da sako na kananan hukumomin Bayelsa sun halarci taron da aka shirya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262