APC Ta Samu Karuwa, Gwamna Diri Ya Kammala Shirin Komawa Jam'iyya Mai Mulki
- Jam'iyyar APC za ta kara yawan gwamnonin da take da su a Najeriya bayan gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ya shirya komawa cikinta
- Gwamna Duoye Diri ya kammala shirye-shiryen komawa jam'iyyar APC, 'yan kwanaki kadan bayan ya fice daga tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP
- Tun bayan ficewarsa daga PDP, Gwamnan na Bayelsa bai sanar da komawa kowace jam'iyya ba, wanda hakan ya sanya aka yi ta canke-canke
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya kammala shirye-shiryen komawa jam’iyyar APC a hukumance.
Gwamna Diri zai koma APC ne a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025, a birnin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Source: Facebook
Wata majiya mai tushe daga sakatariyar APC a Abuja ta tabbatarwa jaridar Daily Trust hakan.
Shettima zai tarbi Diri zuwa APC
Jaridar The Nation ta ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu 'yan kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na APC, za su tarbi gwamnan zuwa jam'iyyar.
Majiyar ta bayyana cewa an riga an kammala dukkan shirye-shirye na tarbar gwamnan daga bangaren shugabancin jam’iyyar na kasa.
Bayan ficewarsa daga jam’iyyar PDP, gwamna Diri ya shafe wasu makonni ba tare da kasancewa cikin kowace jam’iyya ba, abin da ya jawo muhawara da ce-ce-ku-ce a fagen siyasa.
Jiga-jigan jam'iyyar PDP za su koma APC
Majiyar ta bayyana cewa tare da gwamnan, wasu fitattun ‘yan PDP da magoya bayansu a Bayelsa za su shiga APC a rana guda.
“Ya kamata Gwamna Diri ya shiga APC a rana ɗaya da takwaransa na jihar Enugu, Peter Mbah, amma saboda wasu dalilai, an ba shi shawarar ya jira kaɗan duk da cewa ya bar PDP tun da farko."
"Guguwar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC tana nuna yadda ‘yan Najeriya ke gamsuwa da abin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi. Gwamnoni ma suna nuna gamsuwa da manufofinsa.”
"Tattalin arzikin kasa na samun sauyi kamar yadda Bankin Duniya ya tabbatar. Shugaba Tinubu yana aiki tukuru wajen cika alkawurran da ya dauka ga ‘yan Najeriya."
"Saboda haka, gwamnonin jam’iyyun adawa ma suna ganin dacewar su hada kai da gwamnatin tarayya, don ci gaban kasa.”
- Wata majiya

Source: Facebook
Da aka tambayi majiyar ko ba sa jin tsoron mayar da Najeriya karkashin jam'iyya daya, ta bayyana cewa ba za a yi hakan ba.
"Amma muna bukatar karin mambobi. Muna son samun karin gwamnonin jihohi da ‘yan majalisa su shiga jam’iyyarmu. Najeriya ba za ta zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba kawai saboda wasu gwamnoni suna komawa APC."
“Muna da misalai da dama inda kwamishinoni ba su bi gwamna zuwa sabuwar jam’iyya ba.”
- Wata majiya
Sanatan PDP ya koma APC a Bayelsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas a majalisar dattawa, Benson Adagada, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Sanata Benson Adagada ya koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan ya raba gari da tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.
Ya bayyana cewa ya fice daga PDP saboda yadda jam'iyyar ta gaza warware rikicin cikin gida daya dade yana addabarta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

