Jiga Jigai da 'Yan Kwankwasiyya Sama da 600 Sun Watsar da Jar Hula, Sun Koma APC a Kano
- Jam'iyyar APC ta kara takaita NNPP mai mulkin jihar Kano da ta karbi masu sauya sheka sama da mutum 650
- Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hedeija da Jama'are, Rabiu Sulaiman Bichi ne ya jagoranci karbar masu sauya shekar
- Ya yaba masu bisa matakin da suka dauka, yana mai cewa hakan alama ce da ke nuna al'umma na amfana da manufar Renewed Hope
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Aƙalla jiga-jigan NNPP da mambobi 650 sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa sauyin sheƙar ta faru ne a unguwar Gobirawa da ke ƙaramar hukumar Dala, tare da wasu yankuna na Fagge da Ungoggo.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta tattaro cewa yan Kwankwasiyyar sun fice daga jam'iyyar NNPP mai mulkin Kano zuwa APC karkashin jagorancin shugabanninsu a yankin.

Kara karanta wannan
Tinubu ya karbi 'yan majalisa 3 da wasu manyan jiga jigai da suka koma APC a Kaduna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta karbi 'yan Kwankwasiyya 650
Manajan Darakta na Hukumar Raya Kogunan Hadeija da Jama’are, Rabiu Sulaiman Bichi ne ya karbi masu sauya shekar zuwa APC.
Rabi'u ya yaba da matakin da suka ɗauka yana mai cewa hakan ya nuna yadda shugabancin Bola Ahmed Tinubu ke jan hankalin ‘yan Najeriya saboda adalci, haɗin kai da raba romon dimokuraɗiyya.
Ya jaddada cewa Renewed Hope Agenda ta shugaban ƙasa na taka muhimmiyar rawa wajen sauya rayuwar al’umma.
Daga cikin tsare-tsaren da ya ce sun taimakawa al'ummar Najeriya har da ciki har da ahirin ba da lamunin ɗalibai, shirin noma da samar da abinci, da tallafin matasa da mata.
Rabiu Bichi ya kuma bayyana cewa hukumarsa ta yi haɗin gwiwa da bankin noma (BoA) don samar da rancen noma mai sauƙi da nufin bunkasa samar da abinci a ƙasar nan.
A cewarsa:
"APC jam’iyya ce mai adalci da haɗin kai. Muna maraba da ku kamar sauran mambobi, babu bambanci tsakanin tsofaffin mambobi da sababbi.”
Me yasa 'yan Kwankwasiyyan suka bar NNPP?
Da yake jawabi a madadin masu sauya sheka, Ahmad Gobirawa ya ce sun yanke shawarar komawa APC ne bayan ganin nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu daga lokacin da ya hau mulki zuwa yau.
Ya ce suna da tabbacin cewa wannan sauya sheƙar zai ƙara ƙarfafa jam'iyyar APC a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

Source: Getty Images
Taron ya samu halartar jiga-jigan APC, shugabannin al’umma da kungiyoyin matasa, kuma an bayyana shi a matsayin babban ci gaba ga jam’iyyar APC a Kano.
Jigo a NNPP a Kano, Malam Sa'idu Abdu ya shaida wa Legit Hausa cewa cikakken mai akidar kwankwasiyya ba ya iya barinta.
Ya ce wadannan mutanen da ake yadawa cewa sun bar NNPP ba yan kwankwasiyya ba ne, tara su kawai aka yi domin a yaudari jama'a.
Dan siyasar ya ce:
"Duk wanda ya kwankwadi akidar kwankwasiyya ba zai iya fita ba matukar yana kishin talakawa. Wadannan mutane ba namu ba ne, mun san abin da aka shirya.
"Shure-shure dai ba ya hana mutuwa, duk abin da wadannan mutanen yan APC ke yi muna kallonsu, so suke kawai su jawo hankalin jama'a, mu na kara gaya musu da babbar murya Abba sai ka yi takwas In sha Allah."
Kwankwaso ya gargadi masu barin NNPP
A wani labarin, kun ji cewa jagoran jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi gargaɗi ga mutanen da ke barin NNPP da Kwankwasiyya zuwa wasu jam'iyyu.
Kwankwaso ya ce masu ficewa daga NNPP, musamman wadanda ke rike da mukaman shugabanci, za su gane kurensu a zaben 2027.
Tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso ya jaddada cewa siyasarsa ba za ta samu tasgaro ba duk da ficewa da wasu ke yi daga tsarin Kwankwasiyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

