Ta Faru Ta Kare: 'Yan Majalisar PDP 5 a Enugu sun Koma Jam'iyyar APC

Ta Faru Ta Kare: 'Yan Majalisar PDP 5 a Enugu sun Koma Jam'iyyar APC

  • Abubuwa sun kara birkicewa ga jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Enugu bayan wasu 'yan majalisar wakilanta sun sauya sheka
  • 'Yan majalisun guda biyar sun sanar da ficewarsu daga PDP tare da komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya da rinjaye a majalisa
  • Sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka addabi PDP na daga cikin dalilan da suka sanya suka yanke shawarar raba gari da jam'iyyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - ‘Yan majalisar wakilai guda biyar daga jihar Enugu sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar PDP.

'Yan majalisun na tarayya sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki bayan ficewa daga PDP.

'Yan majalisar PDP a Enugu sun koma APC
'Yan majalisar wakilai yayin zaman majalisa Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis, 30 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

APC ta kara karfi, 'yan majalisa 6 daga LP, PDP sun koma jam'iyya mai mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tajuddeen Abbas ya bayyana hakan bayan ya karanta wasikun yin murabus da ‘yan majalisar suka aiko masa daga jam’iyyar PDP.

Wannan lamari ya gudana a gaban Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, wanda ya halarci zaman majalisar a matsayin bako na musamman.

Meyasa suka fice daga jam'iyyar PDP?

A cikin wasikun su, masu sauya shekar sun bayyana cewa sun bar tsohuwar jam’iyyarsu ne saboda rikice-rikicen cikin gida da ba a warware ba, rahoton ya zo a jaridar Vanguard.

Da wannan sauya shekar, jam’iyyar APC yanzu tana da cikakken iko da dukkanin ‘yan majalisar Enugu a majalisar wakilai ta kasa.

Mai magana da yawun sababbin mambobin na APC kuma dan majalisar da ke wakiltar Nkanu ta Gabas/Nkanu ta Yamma, Nnolim Nnaji, ya yi magana da manema labarai bayan sauya shekar.

Dalilin 'yan majalisar na komawa APC

Ya ce sun yanke wannan shawara ne domin su tafi tare da gwamnatin Gwamna Peter Mbah.

Kara karanta wannan

"Laima ta yage,' Sanata Agadaga ya kara ruguza PDP, ya sauya sheka zuwa APC

“Ku zo Enugu ku ga abin da ke faruwa a can. Gwamnanmu yana yin abubuwa masu yawa don al’ummar mu. Mu ma muna son kawo jihar mu kusa da cibiyar mulki.”
“Wannan ba kawai matakin siyasa ba ne, amma babban mataki ne zuwa gaba! Mataki ne na jarumta, hangen nesa, da haɗin gwiwarmu don mayar da Nkanu ta Gabas da Yamma zuwa matakin ɗaukaka.”
“Tsawon lokaci Jihar Enugu ta kasance cikin adawa, tana kallon yadda wasu ke tsara makomar kasa da cin moriyar damar da za su iya inganta rayuwar jama’a."
"Wannan lokacin ya kare! Ba za mu sake zama masu kallo ba lokacin da za mu iya zama masu fadi a ji cikin masu tsara ci gaban Najeriya.”

- Nnolim Nnaji

'Yan majalisar PDP daga Enugu sun koma APC
Shugaban majalisar dattawa, Tajudeen Abbas Hoto: @Speaker_Abbas
Source: Facebook

‘Yan majalisar da suka sauya sheƙa a zaman ranar Alhamis sun haɗa da, Martins Oke, Anayo Onwuegbu, Nnamdi Agbo, Nnolim Nnaji da Mark Obetta

'Dan majalisar PDP ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Maradun II, Maharazu Faru, ya fice daga jam'iyyar PDP.

Maharazu Faru ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai adawa a jihar Zamfara bayan ya bar PDP.

Kara karanta wannan

PDP ta samu koma baya a Zamfara, dan majalisarta ya sauya sheka zuwa APC

Ya bayyana cewa ya fice daga PDP saboda yadda Gwamna Dauda Lawal, ya gaza cika alkawuran da ya dauka lokacin zaben 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng