Shugabancin PDP: Turaki Ya Cike Fam, Ya Bar Sule Lamido da Barazanar zuwa Kotu
- Tsohon Minista, Kabiru Tanimu Turaki ya mika fam na neman zama shugaban jam'iyyar PDP da ake shirin yin zaɓe a kwanakin nan
- Turaki ua mika fam din ne a lokacin da PDP ta hana tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido damar sayen dan domin tsayawa takara
- Tuni ya bayyana shirinsa na tafiya kotu yayin da ita kuma jam'iyyar PDP ta dage tantance ‘yan takara saboda wasu dalilai da suka taso
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ɗan takarar kujerar Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya mika fam ɗin neman tsayawa takara a ofishin kwamitin shirya babban taron jam’iyyar a Abuja.
Turaki, wanda wasu jiga-jigan jam’iyyar suka amince da shi a matsayin ɗan takara na hadin gwiwa, ya kai fam din a ranar Litinin tare da abokansa da magoya bayansa.

Source: Instagram
Daily Trust ta wallafa cewa jam’iyyar PDP ta sanya ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba 2025 domin gudanar da babban taron zaben shugabanninta a birnin Ibadan, Jihar Oyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP: Sule Lamiɗo ya gaza sayen fam
Daily Post ta wallafa cewa kafin Turaki ya kai fam, tsohon Ministan Harkokin Waje kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi yunkurin sayen fam.
Sai dai a lokacin da ya ziyarci sakatariyar PDP da ke Abuja domin sayen fam domin tsayawa takara, amma bai samu jami’an da za su karɓe shi ko sayar masa da fam ba.

Source: Facebook
Sule Lamido, cikin jin fushi, ya shaidawa manema labarai cewa idan har bai samu damar sayan fam ɗin ba, zai iya kai ƙara kotu domin a bi masa hakkinsa.
Sai dai tuni kwamitin shirya babban taron jam’iyyar (NCOC) ya sanar da cewa an dage tantance ‘yan takarar da aka tsara gudanarwa a ranar Talata, 28 ga watan Oktoba, saboda “dalilai bazata."
Jam'iyyar PDP za ta gudanar taro
Shugaban kwamitin NCOC, wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa za a fitar da sabuwar rana nan gaba bayan an cimma matsaya.
A cewarsa:
"Kwamitin ya yi nadamar duk wani rashin jin daɗi da wannan jinkiri ya jawo, amma yana tabbatar wa yan jam’iyyar cewa an ɗauki matakin ne don tabbatar da sahihin taron zabe.”
Ya ƙara da cewa kwamitin na NCOC yana da cikakkiyar niyyar gudanar da babban taron zabe na jam’iyyar cikin gaskiya, lumana da kwanciyar hankali ba tare da wata tangarda ba.
Sule Lamido ya samu matsala a PDP
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana takaicinsa game da yadda aka gudanar da sayen fam na takarar shugaban PDP.
Ya ce ya je hedkwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja, da niyyar sayen fam, amma ya tarar da ofishin a rufe ko kuma babu wanda ke sauraron masu neman takara.
Tsohon gwamna Sule Lamido ya yi gargadin cewa idan ba a samu gyara a tsarin ba, zai dauki matakin shari’a kan jam’iyyar PDP domin kare hakkinsa na wanda ke neman takara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


