Jam'iyyar da El Rufai Ya Koma Ta Rikice, An Kori Shugaban SDP da Wasu Jiga Jigai 2
- A jiya Alhamis, jam'iyyar SDP ta kasa ta kori tsohon shugabanta, Shehu Musa Gabam da wasu manyan jiga-jigai biyu
- Shugabannin SDP na jihohi sun amince da wannan mataki na korar Gabam da sauran wadanda matakin ya shafa
- A cewarsu, sallamar Shehu Gabam daga jam'iyyar ba karamin abin alheri ba ne saboda illar da ya yi wa SDP a lokacin shugabancinsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Shugabannin jam'iyyar SDP na jihohi sun cimma matsaya kan batun korar Alhaji Shehu Musa Gabam, tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) biyu.
Ciyamomin SDP na jihohi 36 da Abuja sun goyi bayan korar shugaban jam'iyyar na kasa, Shehu Gabam bisa zargin aikata manyan laifuffukan almundahana.

Source: Facebook
Ciyamomin SDP na jihohi sun dauki matsaya
Vanguard ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar shugabannin SDP na jihohi kuma shugaban jam’iyyar a Jihar Legas, Femi Olaniyi ya fitar yau Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce sun gamsu da matakin korar jiga-jigan guda uku, kuma suna goyon bayan wannan mataki 100 bisa 100.
Olaniyi ya bayyana cewa saukar Shehu Gabam daga shugabancin SDP a wannan lokaci mai muhimmanci “ya nuna cewa gaskiya ta yi nasara akan mugunta,” yana mai cewa tarihi ba zai manta da illar da ya yi wa jam’iyyar ba.
A cewarsa:
“Korar Shehu Gabam a wannan lokaci ya nuna nasarar masu gaskiya a kan mugaye. Tarihi ba zai manta da irin mulkinsa ba, wanda ya kawo illa ga cigaban siyasar jam’iyyar SDP.
“A wannan lokaci, mu shugabannin SDP na jihohi muna godiya ga kwamitin NWC na ƙasa saboda rawar da suka taka wajen cire Gabam da sauran shugabannin.
"Wannan mataki ya kawo sauƙi ga jam’iyya, kuma muna taya shugabanninmu murna saboda wannan jarumin mataki da zai kare jam’iyyar SDP daga sakarci da barna."
Jam'iyyar SDP ita ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya koma bayan barin APC kuma har yanzu bai fita ya koma jam'iyyar ADC a hukumance ba.

Source: UGC
Me yasa aka kori shugaban SDP?
A tun farko, rikicin jam'iyyar ya ɗauki sabon salo ranar Alhamis, bayan da kwamitin gudanarwa (NWC) ya kori tsohon shugaban SDP na ƙasa, Shehu Gabam, da shugaban matasa, Ogbonna Chukwuma Uchechukwu.
Rahoton The Cable ya ce an kori wadannan jiga-jigai ne bisa zargin rashin da’a, almundahana da cin mutuncin mukamansu.
SDP ta dauki wannan mataki ne a taron NWC da aka gudanar a Abuja bayan wani dogon bincike da matakan ladabtarwa kan shugabannin da abin ya shafa.
PDP ta rabu kan wanda zai zama shugabanta
A wani labarin, kun ji cewa PDP ta fara samun rabuwar kai kan wanda zai oarbi shugabancin jam'iyyar na kasa a babban taron da za a yi a Ibadan

Kara karanta wannan
Atiku da wasu manya na fafutukar fito da shi, shugaban IPOB ya rikita lissafin lauyoyi a kotu
Shugabannin PDP daga yankin Arewa maso Yamma sun nesanta kansu daga amincewar wasu gwamnonin jam'iyya su ka yi da sabon shugaba.
'Yan PDP a yankin Arewa maso Yamma sun ce ba a tuntube su ba kafin sanar da sunan Kabiru Tanimu Turaki, kuma za su fitar da takarda a kan lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

