Jerin Gwamnonin Adawa a Najeriya da Suka Bar Jam’iyyunsu zuwa APC a 2025
Jam'iyyyar APC mai mulki a Najeriya na ci gaba da karbar gwamnonin jam'iyyun adawa wadanda suke sauya sheka zuwa cikinta saboda wasu dalilai.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A cikin shekarar 2025 kadai, akalla manyan gwamnoni uku ne suka bar jam'iyyarsu ta PDP mai adawa a kasar zuwa APC domin ci gaba da ayyukan alheri ga jihohinsu.

Source: Facebook
Rahoton Punch ya ce har yanzu ana hasashen wasu gwamnoni daga jam'iyyar PDP za su shiga APC kafin zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Majiyoyi suka ce hasashen cewa wasu gwamnonin adawa na shirin komawa APC ya yi karfi sosai duk da cewa sun karyata hakan a lokuta da dama.
Daga cikin gwamnonin da aka yi hasashen za su koma APC akwai na Taraba, Agbu Kefas da na Osun, Ademola Adeleke da kuma na jihar Abia, Alex Otti wanda daga baya suka karyata hakan.
Gwamnoni da suka koma APC a 2025
Legit Hausa ta yi duba kan gwamnonin Najeriya uku da suka bar jam'iyyarsu ta PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya da kuma daya da ya yi murabus ba tare da shiga wata jam'iyya ba.
1. Gwamna Sheriff Oborevwori - Delta
Bayan yada jita-jitar sauya sheka da aka yi ta yadawa, gwamnan jihar Delta ya watsar da PDP duk da karyata cewa zai koma APC da ake fada zai yi.
Gwamna Sheriff Oborevwori, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a wani babban sauyin siyasa da ya dauki hankula.
Ya sanar da haka ne a wata ganawar sirri da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Asaba, inda manyan shugabannin APC suka karɓe shi hannu biyu biyu.
Sauyin jam’iyyar ya zo daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauye a siyasar jihar Delta, tare da shirye-shiryen murza gashin baki domin zaɓen 2027.

Source: Facebook
2. Gwamna Umo Eno - Akwa Ibom
Gwamnan da ya biyo bayan na jihar Delta, shi ne gwamnan Akwa Ibom wanda ya yi ta maza ya bar PDP domin tarewa da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Bayan jita-jitar cewa ba zai bar PDP ba, Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya sauya sheka daga jam'iyyar zuwa APC mai mulkin Najeriya a ranar Juma'a 6 ga watan Yunin 2025.
Gwamna Eno ya sanar da haka ne a wani taro na musamnan da aka shirya a fadar gwamnatinsa da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Gwamnonin APC ƙarƙashin jagoranci Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne suka tarbi Fasto Umo Eno a hukumance, cewar rahoton Channels TV.

Source: Facebook
3. Gwamna Peter Mbah - Enugu
A ranar 14 ga watan Oktobar 2025, jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi babban rashi na daya daga cikin gwamnoninta daga Kudancin Najeriya.
Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC daga PDP a taron manema labarai da ya gudana a Enugu.
Peter Mbah ya ce matakin ya biyo bayan dogon tunani ne domin neman hadin kai da gwamnatin tarayya wajen bunkasa jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki zai ba Enugu da yankin Kudu maso Gabas damar samun karin tasiri a gwamnatin Bola Tinubu.

Source: Facebook
4. Gwamna Diri ya yi murabus a PDP
A ranar 15 ga watan Oktobar 2025 ne Gwamna Douye Diri ya tabbatar yin murabus tare da wasu mukarrabansa daga PDP, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Daga bisani, Gwamna Diri ya sauya sheka zuwa cikin ta a hukumance yau Litinin, 3 ga Nuwamba, 2025.
Gwamna Diri, wanda ya bar PDP a watan Oktobar 2025 ya samu tarba daga manyan jagororin APC da magoya baya a birnin Yenagoa.
Dubban magoya bayan APC da na Gwamna Diri daga lungu da sako na kananan hukumomin Bayelsa sun halarci taron da aka shirya.

Source: Twitter
5. Gwamna Sim Fubara - Rivers
Gwamna Siminalayi Fubara ya sanar da sauya shekarsa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki a ranar Talata, 9 ga watan Disamba, 2025.
Fubara ya ce ya yanke shawarar barin PDP ne saboda ta gaza ba shi kariya musamman a rikicin siyasar da ya auku a jihar Ribas.
Wannan sauya sheka na zuwa ne awanni 24 bayan gwamnan ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
6. Gwamna Agbu Kefas - Plateau
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya yi rajistar zama dan APC a hukumance, inda ya karɓi katin jam’iyya daga shugabannin mazaba.
Kefas ya ce rajistar ta zama wajibi domin ya samu cikakken ikon jagorantar harkokin APC da kuma karfafa tafiyar mulki a jihar.
Sauya shekar Kefas na zuwa ne yayin da manyan ‘yan siyasa da ‘yan majalisa a Taraba ke komawa APC gabanin zabuka masu zuwa.

Source: Twitter
7. Gwamna Caleb Mutfwang - Plateau
Jam'iyyar APC mai mulki ta kara yawan gwamnonin da take da su a cikin jihohi 36 na tarayyar Najeriya.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya watsar da jam'iyyarsa ta PDP inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sanar da sauya shekar Gwamna Mutfwang a wajen wani taro.

Source: Facebook
'Gwamnoni 4 za su koma APC' - Fasto
A baya, kun ji cewa babban malamin addinin Kirista, Elijah Ayodele ya yi hasashe game da wasu gwamnonin adawa da ya ce za su iya komawa APC.

Kara karanta wannan
Bayan ganin bidiyon Bello Turji, APC ta hango dalilin alakanta Matawalle da 'yan bindiga
Malamin ya gargadi ga Bola Tinubu cewa wasu gwamnonin adawa za su koma APC amma ba duka ne ke son taimaka masa.
Limamin ya ce wasu daga cikinsu za su shiga jam’iyyar ne kawai don su sami albarkar shugaban ƙasa da kuma neman mukamai.
Asali: Legit.ng



