Jiga Jigan PDP 15 Sun Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar PDP a Zamfara, Sun Fadi Dalili
- Jiga-jigan jam’iyyar PDP 15 a jihar Zamfara, ciki har da shugabanni na jiha da yankuna, sun sauya sheka zuwa APC
- An ce tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, da ministan tsaro, Bello Matawalle, za su shirya bikin tarbarsu
- Sababbin ‘yan APC sun ce sun bar PDP saboda rashin adalci da fifita masu kudi, inda suka yaba da salon jagorancin Yari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Jam’iyyar PDP ta samu babban gibi a jihar Zamfara bayan da jiga-jiganta 15, ciki har da shugabanni na jiha da yankuna, suka sauya sheka zuwa APC a ranar Talata.
Alhaji Tijani Yahaya, wanda ya wakilci tsohon gwamnan jihar kuma sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdul’aziz Yari, shi ne ya karbe su a wani taro da aka gudanar a Abuja.

Source: Twitter
Yari da Matawalle za su karɓe 'yan PDP
Alhaji Tijani ya ce Yari da ministan tsaro, Bello Matawalle, za su shirya babban biki na tarbar sababbin ‘yan jam’iyyar idan suka dawo ƙasar nan ba da jimawa ba, inji rahoton Leadership.
“Yau rana ce mai tarihi ga jam’iyyar mu. Zuwan ku cikin wannan jam'iyya na nufin ƙarfafa tasirin APC da kara ba mu damar lashe zabe a 2027."
- Alhaji Tijani Yahaya.
Ya jaddawa wadanda suka sauya shekar cewa za su damarmakin da ake ba tsofaffin mambobi kuma ba za a nuna masu wariya ba, yana mai kira a gare su da su haɗa kai domin ciyar da APC gaba.
Dalilin ficewar kusoshin PDP zuwa APC
Tsohon jagoran matasa na PDP, Sahad Dabo, ya ce ya bar jam’iyyar ne saboda tana fifita masu hannu da shuni kawai, yana mai cewa salon Abdulaziz Yari ne ya bude masa ido ya gane gaskiya.

Kara karanta wannan
Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC
“PDP ta manta da talakawa. Na shiga APC saboda ina ganin adalci da hangen nesa a cikin jagorancin Yari,” in ji Dabo.
Hajiya Amina Duniya, wacce ta shafe shekaru 25 a PDP, ta yi kira ga shugabannin APC da su tabbatar da adalci da gaskiya, tana mai alkawarin kawo karin magoya baya.

Source: Original
Zamfara: APC ta ce ta na ƙara ƙarfi
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa shugaban APC na Zamfara, Tukur Umar Danfulani, ya yaba da ƙoƙarin Yari da Matawalle wajen ƙarfafa jam’iyyar a jihar.
“Kofar jam’iyyarmu a buɗe take ga kowa. Babu rikici, babu rarrabuwar kai, kuma muna ƙara ƙarfi a kullum,” in ji Yusuf Gusau, mai magana da yawun APC a jihar.
Yusuf Gusau ya ce nasarorin da jam’iyyar ta samu a zaben cike gurbi da yadda manyan mutane ke shiga cikinta, na nuni da cewa APC za ta kwato mulkin Zamfara a 2027.
Martanin APC kan sauya shekar gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, APC ta yi martani ga rade-radin da ke cewa ta fara shirin tarbar Gwamna Dauda Lawal na Zamfara zuwa cikinta.
Wannan ya biyo bayan labarin da ake yayata wa cewa yanzu shiri ya yi nisa na Gwamnan na jihar Zamfara ya sauya sheka.
Kakakin jam’iyyar hamayyar a Zamfara, Alhaji Yusuf Idris, ya ce babu wani kwamiti da aka kafa domin karɓar gwamnan cikin APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

