NNPP Ta Fadi Hadarin Dawo da Zaben 2027 zuwa 2026 a Najeriya
- Jagoran NNPP na yankin Kudu maso Yamma, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya gargadi majalisar dokoki kan shirin dawo da zabe 2026
- Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya ce shirin zai iya dagula tsarin mulki da kawo cikas ga gudanar da gwamnati a fadin kasa baki daya
- Ajadi ya ce ya kamata majalisar kasa ta mayar da hankali wajen karfafa hukumomi maimakon canza jadawalin zaben Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyar NNPP ta bayyana adawarta ga kudirin da majalisar dokokin tarayya ke shirin gabatarwa domin dawo da zaben 2027 zuwa watan Nuwamban 2026.
Jagoran jam’iyyar a yankin Kudu maso Yamma, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, ya ce matakin ba zai amfani kasa ba, domin zai iya haifar da rudani a harkokin siyasa da cikas ga cigaban gwamnati.

Source: Getty Images
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ya ce wannan kudiri da ke cikin dokar gyaran zabe ta 2025 zai iya jefa kasar cikin yanayi na rashin daidaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gargadin 'dan NNPP kan yin zabe a 2026
Ajadi ya bayyana cewa dawo da zabe zuwa 2026 zai sa gwamnati ta kasa gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, domin za a koma cikin yanayin siyasa tun kafin lokacin da ya dace.
Ya ce hakan zai sanya gwamnoni da shugabanni su daina mayar da hankali kan hidimar jama’a, su koma siyasa kafin wa’adinsu ya kare.
A cewarsa:
“Dawo da zabe baya zai lalata tsarin gwamnati. Shugabanni za su bar aiki su koma kamfe, sannan kudin gwamnati za su karkata zuwa harkokin siyasa.
"Najeriya ba za ta iya jure wannan yanayi na siyasa ba.”
Dalilan majalisa da martanin NNPP
Majalisar dokoki ta bayyana cewa dalilinta na wannan kudiri shi ne don baiwa kotuna isasshen lokaci su kammala shari’o’in zabe kafin ranar rantsar da shugabanni a 29 ga Mayu, 2027.
Sai dai Ajadi ya ce wannan hujja ba ta da tushe, domin kammala shari’o’in zabe ya rataya ne a hannun kotuna, ba a kan jadawalin siyasa ba.
Ya tuna cewa a baya ma an taba sauya lokacin zabe daga watan Fabrairu zuwa Maris bisa wasu dalilai, amma hakan bai kawo wani ci gaba ba.
Bukatar karfafa hukumomin gwamnati
Ajadi ya ce abin da kasar ke bukata yanzu shi ne a karfafa hukumomi kamar INEC da kotuna, ba wai a sauya jadawalin zabe ba.
Ya bayyana cewa INEC na bukatar isasshen lokaci don shiryawa, tsara kayan aiki da kuma wayar da kai ga masu kada kuri’a.

Source: Facebook
Daily Post ta rahoto ya ce:
“A maimakon tinkaho da jadawalin zabe, majalisa ta mai da hankali wajen gyara hukumomin da ke kula da zabe da kuma tabbatar da adalci a shari’o’in da suka shafi sakamakon zabe.”
Ajadi ya kuma bukaci majalisar dokoki da ta soke kudirin, yana mai cewa kasar na bukatar nutsuwa da ci gaban tattalin arziki, ba karin rikice-rikice ba.
2027: INEC ta ce za a yi sahihin zabe

Kara karanta wannan
'Paul Biya ya fadi,' Dan Adawar Kamaru da ya yi ikirarin cin zabe zai fitar da sakamako
A wani rahoton, kun ji cewa sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya ce za a yi sahihin zabe a 2027.
Shugaban ya bayyana cewa saboda ingancin zaben da zai jagorata, wanda ya fadi zai taya wanda ya lashe zabe murna.
Legit Hausa ta rahoto cewa Amupitan ya fadi haka ne yayin da ya ke amsa tambayoyi a majalisar dattawa kafin amincewa da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

