"Allah zai Tona Asirinsu": Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano Ya Budewa Kwankwaso Wuta

"Allah zai Tona Asirinsu": Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano Ya Budewa Kwankwaso Wuta

  • Tsohon sakataren gwamnatin Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya kira Rabiu Kwankwaso da Kwankwasiyya da “azzalumai” kuma “marasa mutunci”
  • Ya bayyana haka ne a wani zama da ya yi da magoya bayansa, inda ya ce tsautsayi ne ya kai shi ga yin mu’amala da su Sanata Kwankwaso
  • Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya kuma bayyana yadda wani babban mutum da ya rasu a Kano ya roke shi da kada ya fallasa sirrin Kwankwaso

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya sake zafafa suka kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da mabiyansa na Kwankwasiyya.

A wannan karon, ya bayyana cewa sai da wani babban mutum wanda a yanzu haka Allah Ya yi masa rasuwa, ya roke shi da kada ya fallasa sirrin Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi magana kan munafukai masu son raba shi da Kwankwaso

Abdullahi Baffa Bichi ya dura a kan Kwankwaso
Abdullahi Baffa Bichi, Sanata Rabiu Musa Kwankwas da Gwamna Abba Hoto: AB Baffa/Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A wata hira da Express Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, Dr. Bichi ya bayyana cewa kaddara ce ta sa ya taba shiga mu’amala da Kwankwaso da tsarin Kwankwasiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Bichi ya dura kan Kwankwaso

Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya kara da cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da tsarin Kwankwasiyya zalunci ne kuma mutanen banza ne.

A cewarsa:

“Azzalumai ne, babu abin da su ka iya sai zalunci da karya da damfara, abin da su ka kware kenan, karya, zalunci, damfara da kuma sata.”

Ya kara da cewa wani fitaccen mutum a Kano, wanda yanzu ya rasu, ya taba tambayarsa dalilin da ya kai shi hulda da Kwankwaso.

Abdullahi Baffa Bichi ya kira Kwankwaso azzalumi
Hoton tsohon sakataren gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi Hoto: AB Baffa
Source: Facebook

Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya ce mutumin ya ce:

"Wani babban mutum, Allah Ya yi masa rahama, ya rasu, ya tambaye ni ya ce me ya kai ka hulda da Rabiu...Rabi'u ma ya ce. Me ya kai ka hulda da Rabi'u?"

Kara karanta wannan

Abin da Atiku ya ce wa Kwankwaso da ya cika shekaru 69 a duniya

'Na ce ranka ya dade tsautsayi, ya ce ai ko tsautsayi. Na ce da shi kaddara ce kawai, tsautsayi ne. Ya ce ai tarbiyyarka da tasa ba daya ba ce."

Dr. Bichi ya jaddada cewa Kwankwaso da mabiyansa ba su da gaskiya, yana mai cewa:

“Amma Allah zai tona masu asiri, mutanen Kano za su fahimce su sosai.”

An roki Bichi ya rufa wa Kwankwaso asiri

A cewar Dr. Baffa Bichi, mutumin da ya rasu ya aika masa da tawaga zuwa gidansa domin rokon kada ya fallasa wani abu da zai “bayyana tsiraicin” Kwankwaso da mutanensa.

Ya ce:

“Babban mutum a jihar nan, taso mutane ya yi har gida suka zo suka same ni, ya rasu Allah Ya jikansa, ya ce ya ji, ya ga an nuna masa bidiyo na ce ina da kaza, inda da kaza, ina da kaza.”

Mutumin ya roke shi da cewa:

“Don Allah idan abin da zai bayyana tsiraicinsu ne, suna da 'ya'ya, suna da jikoki, suna da masoya, suna da surukai... idan aka yi haka ba su aka yi wa ba, 'ya'yansu da jikokinsu da al’umma aka yi wa baki daya.”

Kara karanta wannan

Shekara 69: Shugaba Tinubu ya tuna abotarsa da Kwankwaso, ya aiika masa da sako

Dr. Bichi ya ce ya yarda da wannan roko, yana mai cewa:

“Ai mu muna jin maganar magabata, saboda haka babu wani abu na tsiraici da zan saka, duk da dai akwai su, amma na ce ba zan saki ba.”

Gwamnatin Kano ta yi martani ga Bichi

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani mai ƙarfi kan zarge‑zargen da tsohon sakataren gwamna, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, ya yi na cin hanci da rashawa.

Kwamishinan watsa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Garba Waiya, ya ce zargin da Baffa Bichi ya yi “abin takaici ne kuma ya yi ne kawai da niyyar bata wa gwamnatin jihar suna.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya, riƙon amana da hidima ga jama’a, inda ya kalubalanci Abdullahi Baffa Bichi da ya kawo shaida a kan zarginsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng