Wata Sabuwa: 'Yan APC Sun Ja Kunnen Shugaban Jam'iyyar kan Tazarcen Tinubu a 2027

Wata Sabuwa: 'Yan APC Sun Ja Kunnen Shugaban Jam'iyyar kan Tazarcen Tinubu a 2027

  • An fara nuna yatsa ga shugaban APC na kasa kan zargin yana yunkurin hana gwamnan jihar Plateau shigowa cikin jam'iyyar
  • Wata kungiyar masu goyon bayan Bola Tinubu, ta bukaci Farfesa Nentawe Yilwatda da kada ya bari hakan ya kawo matsala ga tazarcen shugaban kasa
  • Kungiyar ta yi gargadin cewa bai kamata son kai ya sanya a jefa tazarcen Shugaban kasa Tinubu a zaben 2027 cikin hadari ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wata kungiyar masu goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a APC mai suna Renewed Hope Advocates of Nigeria (RHAN) ta gargadi shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Yilwatda Nentawe.

Kungiyar ta gargadi shugaban na APC da kada ya bari adawarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ta jefa tazarcen Shugaba Tinubu a zaben 2027 cikin hadari.

Kara karanta wannan

Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC

An ja kunnen shugaban APC na kasa
Shugaba Bola Tinubu da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @aonanuga1956, OfficialAPCng
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Prince Miaphen, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi zargin hana gwamna shigowa APC

Kungiyar RHAN ta nuna babbar damuwa cewa yayin da Shugaba Tinubu da shugabannin APC ke kokarin jan hankalin gwamnonin adawa zuwa jam’iyyar, Nentawe kuma yana kokarin hana Gwamna Mutfwang shigowa APC.

Miaphen ya tunatar da cewa a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jos, karkashin jagorancin Nentawe, an tilasta amincewa da wani kuduri da ke hana Gwamna Mutfwang shiga jam’iyyar.

Ya bayyana wannan matakin a matsayin rashin hangen nesa mai cike da son kai.

“Abin mamaki ne cewa a taron da aka amince Shugaba Tinubu ya yi wa’adi biyu, a lokaci guda kuma aka hana wani gwamna da zai iya zama babban goyon baya ga wannan burin daga shiga jam’iyyar."

- Prince Miaphen

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Yahaya Bello ya bukaci Tinubu kada ya je kamfen a Kogi, ya fadi dalili

Wane gargadi kungiyar ta yi?

Ya yi gargadin cewa wannan mataki na nuna gibin da ke kara fadada tsakanin shugabancin APC na Plateau da hangen nesan Shugaba Tinubu kan siyasar kasa.

Shugaban kungiyar ya bayyana lamarin a matsayin rashin hangen nesa da barazana ga muradun jam’iyya a matakin kasa.

Miaphen ya yi nuni da yadda wasu gwamnonin jihohi irin su Cross River, Ebonyi, Zamfara da Enugu suka yi daidaito da gwamnatin Tinubu.

Ya tambayi dalilin da yasa jam’iyyar za ta nuna adawa da wanda ke son shiga daga Plateau, jihar da ke da masu kada kuri’a sama da miliyan 2.5.

An nuna yatsa ga shugaban APC

Ya zargi Nentawe da son kare takararsa ta gwamna a 2027, yana danganta matsayinsa da bakin ciki kan shan kaye a zaben 2023.

An zargi shugaban APC da hana gwamnan Plateau shigowa jam'iyyar
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Miaphen ya bukaci Shugaba Tinubu da ya shiga tsakani cikin gaggawa, yana mai cewa:

"Plateau jiha ce mai matukar muhimmanci wajen siyasar yankin Arewa ta Tsakiya, kuma bai kamata a rasa ta saboda son kai ba."

Kara karanta wannan

Zaben 2019: Yadda Akpabio ya yi karyar an yi masa magudin zabe a gaban Sanatoci

'Yan ADC za su shigo jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya tabo batun sauya sheka.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa nan bada jimawa ba, wasu manyan jiga-jigai daga jam'iyyar ADC za su shigo APC.

Shugaban na APC ya bayyana cewa tuni shirye-shirye suka kankama don tarbar su zuwa cikin jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng