A Kai Kasuwa: APC Ta Yi Watsi da 'Yunkurin Sauya Shekar' Gwamnan Filato

A Kai Kasuwa: APC Ta Yi Watsi da 'Yunkurin Sauya Shekar' Gwamnan Filato

  • Jagororin jam’iyyar APC Filato sun yi watsi da duk wani yunkurin da aka ce gwamnan jihar yana yi na sauya sheka zuwa cikinta
  • Tuni dai Caleb Gwamna Mutfwang da PDP su ka karyata jita-jitar sauya sheka, suna cewa gwamnan bai da niyyar barin jam'iyyarsa
  • APC ta bayyana cewa idan akwai kamshin gaskiya a labarin, sai dai a kai kasuwa, inda a gefe guda ta fadi matsayarta a kan zaben 2027

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau – Jagororin APC a Jihar Filato sun bayyana cewa ba za su amince da duk wani yunkuri daga Gwamna Caleb Mutfwang na PDP a kan sauya sheka ba.

Wannan matsaya na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da rade-radin sauya shekar wasu gwamnoni daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Zamfara: APC ta fadi gaskiya kan kafa kwamitin sauya shekar gwamna Dauda Lawal

APC ta ce ba ta maraba da Caleb Muftwang
Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang Hoto: Calbe Muftwang
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Crest Hotel, Jos, shugabannin jam’iyyar karkashin sun ce gwamnan bai da gurbi a cikinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta yi watsi da Gwamnan Filato

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jagorancin Farfesa Nentawe Yilwatda sun bayyana matsayarsu bayan Hon. Festus Fuanter ne ya jagoranci kada kuri’a ta murya.

Fuanter ya ce:

“Ba mu bukatar wani ya zo cikin jam’iyyarmu. Muna da kwarin gwiwa cewa za mu lashe zaben 2027 ba tare da taimakon wasu ba.”

Sai dai Gwamnatin jihar Filato ta musanta cewa gwamna Mutfwang bai da niyyar sauya sheka ko rabuwa da jam'iyyarsa.

Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamnan, Gyang Bere, ya ce Mutfwang na tare da PDP kuma yana da kwarin gwiwar sake lashe zabe a 2027.

PDP a jihar ta kuma karyata rade-radin sauya shekar, inda shugaban jam’iyyar na Kudu maso Kudu, Hon. Simon Domle, ya ce PDP ce gadon siyasar Filato.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fadi hanya 1 da APC za ta iya lashe zaben gwamna a jihar Oyo

APC ta na son Tinubu ya zarce

A yayin taron, Farfesa Nentawe ya ce Kiristocin Arewa sun yanke shawarar mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaben 2027, duk da fargaba game da tsarin tikitin Musulmi da Musulmi.

Ya bayyana cewa ayyukan Tinubu sun bayyana shi a matsayin shi na kowa ne, kuma hakan ya sa ba za su ƙi shi ba.

APC na son Tinubu ya yi tazarce
Hoton Shugaban Kasa, Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce:

"Tinubu ya ba kowa dama, Filato yanzu na da murya a kasa."

Daga bisani, jam’iyyar APC ta Jihar Filato ta amince da Tinubu a matsayin ɗan takararta na 2027.

Sanata Simon Lalong ya yaba da matakin, yana cewa Tinubu ya ba da dama ga Filato ta hanyar nadin Farfesa Nentawe a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa.

APC ta ki gwamnan jihar Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC reshen amfara ta bayyana cewa ba ta kafa kowane irin kwamiti da sunan tarbar gwamnan jihar, Dauda Lawal daga PDP zuwa cikinta ba.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta kare ba: Gwamna na iya rasa kujerarsa bayan barin PDP da ta kawo shi

Kakakin jam’iyyar a jihar, Alhaji Yusuf Idris, ya bayyana cewa rahotannin da ake yadawa suna cewa jami’an APC sun fara shirin karɓar Lawal ba su da tushe ballantana makama.

Jam'iyyar da ke mulki a kasa ta bayyana cewa jama'a da ke Zamfara sun daina kaunar Gwamnan da PDP saboda rashin samar da ayyukan da za su ciyar da rayuwarsu gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng