Zamfara: APC Ta Fadi Gaskiya kan Kafa Kwamitin Sauya Shekar Gwamna Dauda Lawal
- Jam’iyyar APC ta Zamfara ta yi martani ga rade-radin da ke cewa ta fara shirin tarbar Gwamna Dauda Lawal zuwa cikinta
- Wannan ya biyo bayan labarin da ake yayata wa cewa yanzu shiri ya yi nisa na Gwamnan na jihar Zamfara ya sauya sheka
- Kakakin jam’iyyar hamayyar, Alhaji Yusuf Idris, ya ce babu wani kwamiti da aka kafa domin karɓar gwamnan cikin APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi watsi da rahotannin da ke cewa tana shirin jawo Gwamna Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya sauya sheƙa zuwa cikinta.
A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar, Alhaji Yusuf Idris, ya fitar a ranar Lahadi, APC ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Yusuf Idris ya jaddada cewa babu wata kwamiti da aka kafa don karɓar gwamnan cikin jam’iyyar.
APC ta karyata shirin sauya shekar Gwamna
The Sun ta ruwaito cewa ba ta taɓa nema ko kusantar Gwamnan jihar Zamfara domin a nemi ya sauya sheka ba.
A cewar Kakakin APC na Zamfara, Yusuf Idris:
“Jam’iyyar APC a Zamfara ba ta taɓa kusantar PDP ko gwamnanta ba domin ta nemi ya shiga jam’iyyarmu."
Yusuf Idris ya ƙara da cewa APC ba ta da wani dalili na neman Dauda Lawal saboda, a cewarsa, gwamnatinsa ta yi rauni sosai kuma ta gaza samun soyayyar al’umma.
APC: Jam'iyyar PDP ta yi rauni a Zamfara
Kakakin ya bayyana cewa APC ba ta taba jin daɗi da irin gazawar da gwamnatin Dauda Lawal ta yi wajen aikin da ya dace a Zamfara.
Ya ce baya ga PDP, jama'ar jihar Zamfara na da wannan ra'ayi, inda su ke takaicin yadda gwamnatin ke aikinta.

Source: Twitter
Yusuf Idris ya tuna cewa da zaben cike gurbi na ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a Kaura Namoda ta Kudu a ranar 16 ga Agusta, 2025, APC ce ta yi nasara.
Ya ce wannan shaida ce da ke nuna cewa APC ke da rinjaye a kan PDP mai mulki, domin a cewarsu, jama’a sun gaji da gwamnati mai ci.
Yusuf Idris ya kuma bayyana cewa ɗan takarar PDP a zaben da wasu daga cikin magoya bayansa sun koma cikin APC bayan gazawar su, yana mai cewa hakan ya nuna raguwar karɓuwar PDP a fadin jihar.
Kakakin APC ya gargadi wasu shafukan yanar gizo da su daina yada labaran ƙarya, yana mai cewa APC ba ta buƙatar yaɗa ƙarya domin ta ƙara samun karɓuwa.
“APC ba ta dogara ga ƙarya don samun farin jini ba, muna kira ga jama’a su rika dogaro da bayanan da ke fitowa kai tsaye daga kafafe nagartattu.”
'Dan takarar PDP ya koma APC
A baya, kun ji cewa Mohammed Lawal, wanda ya tsaya takarar jam’iyyar PDP a zaben cike gurbi na mazabar Kaura Namoda ta Kudu ya sanar da sauya sheka zuwa APC.
Mohammed Lawal ya bayyana cewa ya yi ɗauki wannan mataki ne saboda yadda jam’iyyarsa ta PDP ta nuna masa rashin kulawa, duk da irin gudummawar da ya bata a baya.
Ya sanar da haka ne a Gusau, inda ya yaba da manufofin APC, yana mai cewa jam’iyyar ta fi dacewa da burinsa na tallafa wa ci gaban jihar Zamfara nan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


