Ado Doguwa Ya Kwararo Yabo ga Kwankwaso da Suka Hadu a Majalisar Wakilai
- 'Dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya yabawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bisa jagoranci da halayen kirki
- Doguwa ya bayyana cewa kulawar Kwankwaso ta taimaka masa wajen yin aiki cikin natsuwa a majalisa a lokacin aikinsu tare
- Yabon na Doguwa ya biyo bayan zaman girmamawa ga tsohon shugaban majalisa, marigayi Agunwa Anaekwe a majalisar wakilai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Dan majalisar wakilai mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya yabawa jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ado Doguwa ya yaba wa Kwanwaso ne bisa irin jagoranci, tawali’u da kulawa da nuna ga abokan aikinsa a lokacin da ya ke mataimakin shugaban majalisa.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan abubuwan da Doguwa ya fada ne a wani bidiyo da Saifullahi Hassan ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Doguwa, da dan APC ne, ya yi wannan yabo ne yayin zaman karramawa da majalisar wakilai ta yi domin tunawa da tsohon shugaban majalisar, marigayi Rt. Hon. Agunwa Anaekwe.
Ado Doguwa ya yaba wa Rabiu Kwankwaso
A yayin jawabin nasa, Doguwa ya bayyana yadda Kwankwaso ya nuna masa kulawa lokacin da su ke aiki tare a majalisa.
Ya yi magana yana mai cewa hakan ya taimaka masa wajen gudanar da aikinsa cikin kwanciyar hankali da natsuwa.
Doguwa ya ce a lokacin da suke majalisa tare, Sanata Kwankwaso wanda yake mataimakin shugaban majalisa ne, ya ba shi damar tafiya taro a Benin tare da sabuwar amaryarsa, Halima.
Ya bayyana cewa Kwankwaso ya ba shi damar samun kujerun jirgi biyu domin tafiya Benin tare da amaryarsa.
Manyan da suka hallara majalisa
Taron da aka gudanar a harabar majalisar dokokin tarayya ya samu halartar shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.

Kara karanta wannan
Surukar Akpabio ta ballo ruwa, ta jingina Shugaban Majalisa da kashe jama'a a Akwa Ibom
Tajudeen Abbas ya gabatar da Sanata Kwankwaso a matsayin tsohon mataimakin shugaban majalisa, tsohon gwamnan Kano, kuma jagoran jam’iyyar NNPP.
Haka kuma, tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya halarci zaman kamar yadda ya wallafa a X.
Tambuwal ya bayyana marigayi Anaekwe a matsayin shugaba mai jajircewa da ya taka rawar gani wajen kafa ginshikin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Source: Facebook
Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, yana mai cewa tarihin majalisar dokoki ba zai cika ba tare da ambaton gudummuwar Anaekwe ba.
Jawabin mataimakin shugaban majalisa
A nasa bangaren, mataimakin shugaban majalisa, Hon. Benjamin Kalu, ya bayyana marigayi Anaekwe a matsayin mutum mai nagarta wanda ya yi shugabanci cikin gaskiya.
Kalu ya ce:
“A lokacin yana da shekara 36 kacal, amma ya dauki nauyin kare darajar dimokuraɗiyya da kishin kasa.
Ko da mulkinsa bai daɗe ba, amma al’amarin ya zama abin koyi ga kowane dan siyasa.”
Taron ya kuma samu halartar wasu tsofaffin ‘yan majalisa, iyalan marigayi Anaekwe, da ma’aikatan majalisar daga zangon 1992–1993.
'Dan APC ya yi magana kan Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa wani dan jam'iyyar APC a jihar Kano, Garba Kore ya tabbatar da cewa Kwankwaso ya fi su jama'a.
Sai dai duk da haka, Garba Kore ya ce yana da tabbas za su kwace mulkin jihar daga hannun Abba Kabir a 2027.
'Dan siyasar ya bayyana cewa da karfi za su kwace mulkin Kano a 2027 ba tare da jin tsoron wani abu da zai iya biyo baya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

