Ana Wata ga Wata: Matsala Ta Tunkaro Gwamna Diri kan Ficewa daga PDP

Ana Wata ga Wata: Matsala Ta Tunkaro Gwamna Diri kan Ficewa daga PDP

  • Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ya raba gari da jam'iyyar PDP wadda ya lashe zabe har sau biyu a kakashinta
  • Ficewarsa daga PDP ya sanya an fara hasashen cewa yana iya tattara komatsansa zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Sai dai, Kenneth Okwonko ya kawo dalilan ya kamata su sanya gwamnan na Bayelsa ya rasa kujerarsa gaba daya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan siyasa a jam’iyyar ADC kuma fitaccen ɗan wasan Nollywood, Kenneth Okonkwo, ya tabo batun ficewar gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, daga jam'iyyar PDP.

Kenneth Okonkwo ya bukaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta ayyana kujerar Gwamna Douye Diri, a matsayin wacce ta zama babu kowa a kai, bayan ya fice daga PDP.

An bukaci INEC ta karbe kujerar Gwamna Diri
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri. Hoto: Duoye Diri
Source: Twitter

Kenneth Okonkwo ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Instagram.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Fayose ya fadi gwamnonin da za su rage a jam'iyyar Jam'iyyar PDP

Gwamna Diri ya yi murabus daga PDP

Gwamna Diri ya sanar da ficewarsa daga PDP tare da wasu mambobin majalisar dokokin jihar Bayelsa a ranar Laraba, 15 ga watan Oktoban 2025.

Hakan ya janyo hasashen cewa zai iya komawa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa ya yi murabus daga jam’iyyar ne saboda wasu dalilai, sai dai bai yi cikakken bayani ba kan matsalolin da suka sanya ya yanke wannan shawarar.

Haka kuma, bai ambaci ficewar mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, a cikin sanarwarsa ba.

An bukaci INEC ta karbe kujerar Gwamna Diri

A rubutun da ya yi, Kenneth Okonkwo ya jaddada cewa Gwamna Diri ya rasa cancantarsa ta ci gaba da zama gwamna domin ya fita daga jam’iyyarsa kuma yanzu ba ya cikin kowace jam’iyyar siyasa.

Kenneth Okonkwo ya ambaci sashe na 177(c) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ya tanadi cewa mutum zai cancanci yin takarar kujerar gwamna ne idan yana ɗan jam’iyya kuma jam’iyyar ta tsayar da shi takara.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya hango jihohin da za su koma karkashin APC kafin karshen 2026

Ya ce saboda haka, INEC ta gaggauta ayyana kujerar a matsayin wadda babu kowa a kai, sannan ta shirya sabon zaɓen gwamna cikin kasa da watanni uku.

Kenneth Okonkwo ya bukaci a karbe kujerar Gwamna Diri
Dan siyasa kuma jarumin Nollywood, Kenneth Okonkwo. Hoto: Kenneth Okonkwo
Source: Twitter
“Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya bar kujerarsa ta gwamna ta hanyar ficewa daga PDP, da rashin kasancewa cikin kowace jam’iyya."
“Dokar kasa ta bayyana a fili cewa dole ne kowane mutum da aka zaɓa a wani mukamin gwamnati, ya kasance ɗan jam’iyya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada a sashe na 177(c).”
“Gwamna Diri, saboda rashin kasancewa cikin kowace jam’iyya, ya rasa kujerarsa ta gwamna. Wanda aka zaɓa zai iya sauya jam’iyya daga wata zuwa wata, amma ba zai taɓa zama marar jam’iyya ba.”
“Saboda haka, ina kira ga INEC ta gaggauta ayyana kujerarsa a matsayin fanko kuma ta gudanar da sabon zaɓen gwamna a jihar Bayelsa cikin kwanaki 90 masu zuwa."
- Kenneth Okonkwo

Sanatan PDP ya koma jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta rasa daya daga cikin sanatocin da take da su a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Wike ya yi shagube ga masu sauya sheka daga PDP zuwa APC duk da yana tare da Tinubu

Sanata Samaila Dahuwa Kaila wanda ke wakiltar Bauchi ta Arewa ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka addabi PDP na daga cikin dalilan da suka sanya ya fice daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng