LP ko ADC?: Peter Obi Ya Fadi Yadda Ƴan Adawa Za Su Kayar da Tinubu a Zaben 2027
- Peter Obi ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, domin yana da kwarewar shugabantar Najeriya
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kuma bayyana cewa zai iya canza Najeriya cikin shekaru hudu idan ya lashe zabe
- Game da jam'iyyar da zai yi takara, Obi ya bayyana hanya mafi sauki ta kayar da Shugaban kasa Bola Tinubu a zabe mai zuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya ba da tabbacin cewa zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa.
Peter Obi ya kuma ba 'yan Najeriya tabbacin cewa zai canza kasar nan ta fuska mai kyau cikin shekaru hudu kacal idan aka zabe shi a 2027.

Source: Facebook
Peter Obi zai tsaya takarar shugaban kasa?
'Dan takarar shugaban kasa a 2023, karkashin jam'iyyar LP, ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a Abuja, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan, ya bayyana cewa yana da duk wata kwarewa da ake bukata ta yin jagoranci, don haka, 'yan Najeriya ba za su yi nadamar zabarsa ba.
"Kwarai zan tsaya takara, kuma za a ga sunana a takardun kada kuri'a. Ya kamata mutane su kalli 'yan takarar, su ga wa ya fi kwarewa, wanda zai iya cire A'i daga rogo.
"Ni ina ganin na cancanta; ina da duk wata kwarewa ta gudanar da shugabanci. Zan sake maimaitawa cewa, a cikin shekara hudu, zan sauya Najeriya ta fuska mai kyau."
- Peter Obi.
LP ko ADC?: Peter Obi ya hango nasara
Peter Obi dai ya tsaya takara a 2023 a ƙarƙashin LP, amma yanzu yana cikin ƙungiyar haɗakar ‘yan adawa da ta rungumi ADC a matsayin jam'iyyar ta a zaben 2027.
Sai dai ya jaddada cewa har yanzu shi mamba ne na jam'iyyar LP, kuma zai ci gaba da aiki tare da sauran shugabannin adawa domin ceto Najeriya daga jagoranci marar nagarta.
Da aka tambaye shi ko zai koma PDP, Obi ya ce:
“Mu duka za mu haɗu a matsayin ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa. Lokaci ya yi da za mu haɗu domin ceto ƙasar nan daga matsalolin da take ciki.”
Obi ya yi nuni da cewa idan 'yan adawa suka hada kansu, to za su iya kayar da Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC a zabukan 2027 masu zuwa.

Source: Twitter
Obi ya soki sauya shekar gwamnonin PDP
Obi ya bayyana damuwa kan sauya shekar gwamnonin Enugu da Bayelsa zuwa APC, yana mai cewa irin wannan hali ba zai taimaka wajen gina dimokuradiyya ba.
“Ba mulkin soja ake yi ba. Siyasar dimokuradiyya tana bukatar lallashi, ba tursasawa mutane ba,” in ji Obi.
Ya kara da cewa koda yake Gwamna Peter Mbah abokinsa ne, “amma ya yanke shawarar komawa APC ne bisa ra’ayinsa na siyasa.”
Obi ya jaddada cewa ba za a iya ‘kwace’ yankin kudu maso gabas ta siyasa ba, domin jama’ar yankin sun riga da sun san inda ke masu ciwo.
'Obi ne kadai mai karfi a adawa' - Fayose
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Peter Obi ne kadai mai sauran karfi da tasiri a cikin ƴan adawa a Najeriya, cewar tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose.
Tsohon gwamnan na Ekiti ya bayyana cewa duk da Obi na da karfin fada a ji a bangaren adawa, ba zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027 ba.
Ya bayyana cewa sauran manyan ‘yan adawa kamar Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, sun rasa amincewar jama’a, yana mai cewa, mutane sun daina sauraron su kamar da.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


