Ta Faru Ta Kare: Fayose Ya Fadi Gwamonin da Za Su Rage a Jam'iyyar PDP

Ta Faru Ta Kare: Fayose Ya Fadi Gwamonin da Za Su Rage a Jam'iyyar PDP

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi tsokaci kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
  • Fayose ya bayyana cewa yawan gwamnonin da jam'iyyar PDP take da su zai ci gaba da raguwa nan bada jimawa ba
  • Tsohon gwamnan ya wanke Shugaba Bola Tinubu daga zargin yana da hannu a rikicin da ya dade yana addabar PDP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana kan ficewar da wasu gwamnoni ke yi daga jam'iyyar PDP.

Ayodele Fayose ya bayyana cewa akwai gwamnoni uku da aka zabe su a karkashin PDP da za su bar jam’iyyar nan ba da jimawa ba.

Fayose ya yi magana kan rikicin PDP
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayode da tambarin jam'iyyar PDP. @GovAyoFayose, @OfficialPDPNig
Source: Facebook

Fayose ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya ƙi karbar tayin muƙami daga Shugaba Tinubu, ya faɗi dalilansa

An yi tattaunawar ne jim kadan bayan gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya sanar da ficewarsa daga PDP.

Me Ayo Fayose ya ce kan rikicin PDP?

A cewarsa, jam’iyyar adawa ta PDP na iya samun kanta da gwamnoni biyar kawai sakamakon rikice-rikicen cikin gida da ke ci gaba da addabar ta.

"Zan gaya muku gaskiya, akwai wasu gwamnoni uku da za su bar jam’iyyar nan ba da jimawa ba."
"Za a rage saura biyar, kuma daga cikin biyar ɗin nan, ɗaya daga cikinsu zai yi ta fama wajen neman tikitin jam’iyyar, domin wannan tikitin ba ya da wata kima, kamar takarda ce kawai."

- Ayodele Fayose

Ya zargi wasu gwamnoni na PDP da haifar da koma baya ga jam’iyyar saboda son karɓe cikakken iko da jagoranci a cikinta.

“Su ne ke lalata jam’iyyar saboda son karɓe iko gaba ɗaya. Hakan ne ya faru a shekarar 2023."

- Ayodele Fayose

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya hango jihohin da za su koma karkashin APC kafin karshen 2026

Fayose ya wanke Shugaba Tinubu

Fayose ya yi watsi da zargin cewa Shugaba Bola Tinubu yana tilasta wa gwamnoni na jam’iyyun adawa su koma APC, yana mai cewa mafi yawansu suna sauya sheka ne saboda kare muradunsu da lissafin siyasa.

Fayose ya wanke Tinubu kan rikicin PDP
Ayodele Fayose tare da Mai girma Bola Tinubu. Hoto: @GovAyoFayose
Source: Twitter
“Ba za a dora wa Shugaba Tinubu laifin matsalolin PDP ba. PDP ta kamu da ciwo mai tsanani kuma babu maganinsa."

- Ayodele Fayose

Tsohon gwamnan ya kara jaddada cewa rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi, ya faru ne sakamakon cin amanar juna daga shugabanninta.

“Wadanda suka hallaka jam’iyyar sun san kansu. Akwai bambanci tsakanin tsohon gwamna da wanda yake kan mulki."

- Ayodele Fayose

Ko da yake har yanzu yana da katin zama ɗan jam’iyyar PDP, Fayose ya ce ba shi da alhakin gyara rikicin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa shugabannin yanzu ne ya kamata su ɗauki alhakin abin da ke faruwa.

Sanata ya fice daga PDP zuwa APC

Kara karanta wannan

Wike ya yi shagube ga masu sauya sheka daga PDP zuwa APC duk da yana tare da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa a majalisar dattawa, Samaila Dahuwa Kaila ya fice daga jam'iyyar PDP.

Samaila Dahuwa Kaila ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan ya rabu da PDP wadda ya lashe zabe a karkashinta a shekarar 2023.

Sanatan ya bayyana cewa ya fice daga jam'iyyar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka addabe ta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng