Wike Ya Yi Shagube ga Masu Sauya Sheka daga PDP zuwa APC Duk da Yana Tare da Tinubu

Wike Ya Yi Shagube ga Masu Sauya Sheka daga PDP zuwa APC Duk da Yana Tare da Tinubu

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan sauya shekar da wasu 'yan siyasa ke yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Wike ya bayyana masu yi sukar salon siyasarsa yanzu su ne su ke komawa jam'iyyar APC mai mulki
  • Ministan ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan manufofin da ya ke aiwatarwa a gwamnatinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya mayar da martani ga masu sukar yanayin siyasarsa.

Wike ya bayyana cewa yawancin wadanda suka taba zarginsa da taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC yanzu suna ta komawa jam’iyyar da kansu.

Wike ya yi wa 'yan PDP shagube
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Wike ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, yayin da yake kaddamar da aikin gina babban titin Outer Southern Expressway (OSEX) daga Ring Road 1 zuwa Ring Road 2 a kan titin Wassa, Abuja.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya hango jihohin da za su koma karkashin APC kafin karshen 2026

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan jawabin nasa ya zo ne rana guda bayan gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Me Wike ya ce kan masu komawa APC?

A cewar Wike, siyasar da yake yi ta tabbatar da gaskiyarsa, yana mai cewa siyasa ba ta dace da masu zuciya mara natsuwa ba, labarin ya zo a Punch.

"Na dade ina kallon talabijin da kuma kafafen sada zumunta. Wadanda suka taba zargi na da rushe jam’iyyar PDP da taimaka wa APC, su duka yanzu suna APC."
"Idan har gaskiya ne cewa na yi wa APC aiki, to kamata ya yi su yaba min, ba su zarge ni ba. Domin hakan yana nufin na yi musu aiki nagari.”

- Nyesom Wike

Wike ya kuma jaddada biyayyarsa ga Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa manufofin gwamnatinsa, musamman cire tallafin man fetur, sun kawo gagarumin canji a harkokin kudi na jihohi da birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

PDP ta aika sako ga Tinubu bayan Gwamna Mbah ya sauya sheka zuwa APC

Wike ya yabawa Shugaba Tinubu

Ya bayyana cewa lokacin da yake gwamna, yana fama da neman rance daga bankuna domin gudanar da ayyukan gwamnati da biyan albashi, amma yanzu lamura sun sauya saboda shugabancin Tinubu.

“Na yi gwamna na tsawon shekaru takwas. Na san yadda ake shan wuya a nemi rance domin ayyuka da biyan albashi."
"Amma yau saboda jagoranci mai hangen nesa na shugaban kasa, bankuna ne suke bin jihohi suna neman su karɓi kudi."
"Ana biyan albashi, ana yin ayyuka, babu gwamnan da yake magana kan barin bashi ga wanda zai gaje shi. Wannan shi ne jagoranci mai hangen nesa.”

- Nyesom Wike

Wike ya yabawa Mai girma Bola Tinubu
Nyesom Wike na jawabi a wajen taro. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Facebook

Wike ya ce, ci gaba da ayyukan samar da ababen more rayuwa da ake gani a Abuja a yanzu yana da nasaba kai tsaye da jagoranci da tsari na Shugaba Tinubu.

"Duk abin da ake gani a yau a Abuja, sakamakon irin wannan shugabanci ne. Idan aka kafa tsari mai kyau, duk wanda aka nada zai bi tafarki mai kyau.”

Kara karanta wannan

"Ba siyasa ba ce": Jagoran APC ya kare yafiyar Tinubu ga masu manyan laifuffuka

- Nyesom Wike

Gwamnonin da suka rage a PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa yawan gwamnonin da jam'iyyar PDP take da su sun ragu a jihohin Najeriya.

Yawan gwamnonin ya ragu zuwa kasa da guda 10 bayan ficewar gwamnonin jihohin Enugu da Bayelsa.

A yanzu gwamnoni biyar ne kawai suka rage a jam'iyyar PDP daga jihohin da ke yankin Arewacin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng