Bayan Ficewar Peter Mbah zuwa APC, Gwamnan PDP Ya Sake Yin Murabus
- Kwana daya bayan sauya shekar gwamnan Enugu daga PDP, takwaransa daga jam'iyyar hamayyar ya yi murabus daga cikinta
- Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya sanar da barinsa jam’iyyar PDP a wani taro da aka gudanar a gidan gwamnati ranar Laraba
- Kakakin majalisar jihar, Rt Hon. Abraham Ngobere, da wasu ‘yan majalisa 18 na PDP suma sun bi sawunsa wajen yin murabus daga jam’iyyar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yenagoa, Bayelsa - Jam'iyyar PDP ta kuma samun nakasu bayan gwamna mai ci ya yi murabus daga cikinta.
Gwamna Douye Diri na Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP, ya sanar da hakan a ofishinsa da ke gidan gwamnati.

Source: Facebook
A wani bidiyo da shafin gwamnan ya wallafa a Facebook, gwamnan ya sanar da ficewarsa a yau Talata 15 ga watan Oktoban shekarar 2025 a birnin Yenagoa da ke jihar.

Kara karanta wannan
'Babu sauran hamayya,' Jam'iyyar APC ta tsaida ɗan takararta a zaben gwamnan Ekiti
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Diri ya watsar da PDP zuwa APC
Wannan murabus ya faru ne bayan gwamnan Enugu, Peter Mbah ya koma APC, wanda ya rage wa PDP gwamnoni takwas kawai.
Gwamna Peter Mbah ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC daga PDP a taron manema labarai da ya gudana a Enugu.
Mbah ya ce matakin ya biyo bayan dogon tunani ne domin neman hadin kai da gwamnatin tarayya wajen bunkasa jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki zai ba Enugu da yankin Kudu maso Gabas damar samun karin tasiri a gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamnan PDP ya yi murabus daga jam'iyyar
Kakakin majalisar jihar Bayelsa, Abraham Ngobere da ‘yan majalisa 18 na PDP sun yi murabus tare da gwamna Douye Diri daga jam’iyyar adawa.
Yin murabus din gwamnan ya biyo bayan samun goyon bayan yan majalisu 23 daga jihar karkashin jagorancin kakakin majalisar, cewar rahoton Channels TV.
Ana sa ran gwamnan zai sanar da jam'iyyar da zai shiga nan ba da jimawa domin ci gaba da ayyukan alheri a jihar.
A cikin wani bidiyon da aka wallafa, Gwamna Diri ya ce ba shi kadai zai bar jam'iyyarsa ba.
Ya ce:
"Ba zan yi murabus ni kadai ba, kamar yadda ku ke gani ina tare da kakakin majalisa da mataimakinsa na PDP da za su bi ni.
"Akwai wadanda ba su nan saboda sun tafi gudanar da harkokin mulki a hukumance da aka tura su.
"A yau, na yi murabus daga jam'iyyar PDP saboda wasu bayyanannun dalilai, ina godiya ga abokai na da magoya baya na da suka kasance da mu."
A karshe, gwamnan ya bayyana cewa idan suka hada kai za su gina jihar Bayelsa da kuma inganta Najeriya baki daya.
Gwamnonin da ake hasashen za su koma APC
A baya, mun ruwaito muku cewa akwai wasu gwamnonin jam'iyyun adawa da ake hasashen za su koma APC mai mulkin Najeriya.
Alamu na nuna cewa jam'iyyar APC za ta samu karin gwamnoni uku da za su baro tsagin adawa zuwa cikinta a mako mai zuwa.
Rahotanni sun gano sunayen gwamnoni biyu daga ciki yayin da Gwamna Peter Mbah da ya riga ya koma APC daga PDP.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

