2027: Babban Dan APC Ya Fadawa Duniya cewa za Su Kwace Kano daga hannun Abba
- Garba Kore na jam’iyyar APC ya ce za su kwace mulkin Kano daga hannun Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a 2027
- Yayin da ye ke bayani, ya amince cewa Rabiu Kwankwaso ya fi su jama’a kuma ya san ba za su ci zaben gaskiya ba
- A ikirarin da ya yi, Garba Kore ya ce a Najeriya idan mutum ya karya doka amma yana da ƙarfi, ba a yi masa hukunci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Fitaccen 'dan jam’iyyar APC a Kano, Garba Kore, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bayyana a fili cewa jam’iyyarsu za ta kwace mulkin jihar.
Sanannen 'dan siyasar ya yi ikirarin cewa za su kwace mulki daga hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a zaben 2027.

Source: Facebook
Garba Kore ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, da Amb Funtua ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu mamaki an dauko wannan ne daga hirar da aka yi da 'dan siyasar a gidan rediyo.
Garba Kore: Za mu kwace Kano a 2027
Kore ya bayyana cewa jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya fi su jama’a a Kano, amma hakan ba zai hana su samun mulki ba.
Ya ce ya san ba za su ci zabe na gaskiya ba, amma za su kwace mulki, saboda haka rayuwar siyasa take a Najeriya.
Lokacin da aka tambaye shi ko wannan ya saba wa doka, sai ya amsa da cewa:
“A Najeriya idan ka samu dama, ka karya ta karya abin ka kawai. Idan baka da ƙarfi, ne kawai za a hukunta ka.”
Magana kan sabon shugaban INEC
A yayin da yake magana kan jita-jitar cewa nadin shugaban hukumar zabe (INEC) na da alaka da shirin taimaka wa APC, Garba Kore ya ce ba shi da shaida kan hakan.
Sai dai duk da haka, Kore ya kara da cewa idan aka ce haka ne, zai iya yarda duk da ba shi da wata hujja karara.
Ya ce tuni suka shirya dabaru daban-daban da za su tabbatar da dawowar APC kan mulki a jihar Kano.
Kore ya bayyana cewa abubuwan da ya taba faɗa a baya game da siyasar Kano sun tabbata, kuma shi ya san hakan tun farko.
Bayanin Kore kan rikicin masarautar Kano
Garba Kore ya kuma yi tsokaci kan rikicin masarautar Kano, inda ya ce batun ba na kotu ba ne, yana da nasaba da siyasa da ikon gwamnati.
A cewarsa, abin da ke faruwa a masarautar yanzu ya tabbata kamar yadda ya taɓa faɗi a baya, kuma hakan zai ci gaba da gudana.
Ya ce hanya mafi sauƙi ga ‘yan Kwankwasiyya ita ce su dawo cikin jam’iyyar APC domin samun riba a siyasa.

Source: Twitter
Abba Kabir ya yi magana kan zaben 2027
A wani labarin, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan zaben 2027 da tazarcen da ya ke fatan yi.
Gwamnan ya yi magana ne a daidai lokacin da ake masa barazana ta hanyoyi daban daban kan samun wa'adi na biyu.
Duk da barazanar da ya ke fuskanta, Abba Kabir Yusuf ya ce da Allah ya dogara wajen fuskantar siyasar 2027 ba mutane ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


