Lamura na Kara Lalacewa a PDP, Jam’iyyar Ta Dakatar da Shugabanninta na Jihohi

Lamura na Kara Lalacewa a PDP, Jam’iyyar Ta Dakatar da Shugabanninta na Jihohi

  • Kungiyar shugabannin jam’iyyar PDP a jihohi ta dauki mummunan mataki kan wasu daga cikin mambobinta
  • Shugabannin adawar sun dakatar da jagorori biyu daga Abia da Imo bisa zargin ayyukan cin amanar jam’iyya
  • An zargi shugabannin da hadin baki da wasu da aka alakanta da APC don kawo cikas ga babban taron jam’iyyar da ke tafe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar shugabannin jam’iyyar PDP a jihohi ta yi taro na musamman a Abuja domin duba kan halin da jam'iyyar ta shiga.

Yayin taron, kungiyar ta dakatar da shugabanninta biyu daga jihohi saboda zargin ayyukan da suka saba wa manufofin jam’iyyar PDP.

Jam'iyyar PDP ta dakatar da shugabanninta a jihohi
Shugabannin Imo da Abia da shugaban PDP, Umar Damagum. Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria.
Source: Facebook

An dakatar da shugabannin PDP 2 a jihohi

An cimma wannan matsaya ne a wani taro da jam'iyyar ta wallafa a Facebook wanda aka gudanar a ofishin PDP na Abuja ranar Talata 14 ga watan Oktoban 2025

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama miji da mata masu safarar makamai ga ƴan ta'adda a jihohin Arewa

An gudanar da taron ne karkashin jagorancin Edward Percy Masha wanda shi ne sakataren riko na kungiyar.

Har ila yau, kungiyar shugabannin na zargin wadanda aka dakatar da ƙoƙarin kawo tangarda ga babban taron jam’iyyar mai zuwa.

Shugabannin da aka dakatar su ne Austine Nwachukwu wanda shi ne shugaban PDP na Imo, da kuma Amah Abraham Nnana, shugaban PDP na Abia.

Kungiyar ta zargi mutanen biyu da yin haɗin baki da ake dangantawa da jam’iyyar APC domin kawo cikas ga shirye-shiryen babban taron PDP da aka shirya gudanarwa daga 15 zuwa 16 ga Nuwamba.

PDP ta fara daukar matakai kan masu ci mata amana
Shugaban jam'iyyar PDP ta kasa, Umar Damagum a Abuja. Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria.
Source: Twitter

PDP ta yi nade-naden mukamai a Abuja

Sanarwar, wadda shugaban PDP a Edo, Tony Aziegbemi da Edward Percy Masha suka sanyawa hannu, ta kuma tabbatar da nadin Tony Aziegbemi a matsayin sabon shugaban kungiyar shugabannin PDP na jihohi.

Kungiyar ta tattauna batutuwan da suka shafi haɗin kai da zaman lafiya cikin jam’iyyar, matsin lamba daga jam’iyyar mai mulki, da kuma shirye-shiryen babban taro.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda ana batun sulhu a Katsina, mutum 12 sun kwanta dama

Ta kuma zargi jam’iyyar APC da yin ƙoƙarin siyasa da babu dimokuraɗiyya ta hanyar matsa wa gwamnoni, ‘yan majalisa da sauran manyan ‘yan PDP don su koma APC.

Sanarwar ta ce:

“Wannan dabi’a ta APC na nuni da yunƙurin lalata tsarin dimokuraɗiyya da kafa jam’iyya ɗaya a ƙasar nan.”

Kungiyar ta nuna goyon bayanta ga kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), kungiyar gwamnoni ta PDP da sauran kwamitocin jam’iyyar.

Haka kuma ta jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki tare da shugabancin PDP don sake ginawa da ƙarfafa jam’iyyar a matsayin ingantacciya a zaben 2027 mai zuwa.

'Yan majalisa 3 sun fice daga PDP zuwa APC

A wani labarin, Shugaban majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya karanto wasikun wasu ‘yan majalisar wakilai uku daga Kaduna, na sauya shekarsu daga PDP zuwa APC.

An ce Gwamna Uba Sani ya halarci zaman majalisar don marabtar ‘yan majalisar zuwa APC, lamarin da ya nuna tasirinsu a siyasar Kaduna.

Sauya shekar 'yan majalisar ta raunana PDP a Kaduna, yayin da APC ke kara karfi a majalisar wakilai da kuma Arewa maso Yamma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.