APGA: Yadda Tsoron EFCC ke Kora Gwamnoni, 'Yan Adawa zuwa APC

APGA: Yadda Tsoron EFCC ke Kora Gwamnoni, 'Yan Adawa zuwa APC

  • Tsohon Shugaban APGA, Cif Chekwas Okorie ya yi bayanin abin da ke kora gwamnonin adawa zuwa cikin jam'iyya mai mulki ta APC
  • Tsohon shugaban, wanda ya zama jagoran APGA na farko ya ce ‘yan siyasa suna amfani da jam’iyya mai-ci matsayin mafaka daga hukunci
  • Okorie ya ce duk da haka, Najeriya ba za ta taɓa zama ƙasar da ke ƙarƙarshin jam’iyyar siyasa ɗaya ba saboda bambancin da ke cikinta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban farko na jam’iyyar APGA, Cif Chekwas Okorie, ya caccaki yadda gwamnoni da dama ke sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa zuwa APC.

Ya bayyana cewa gwamnonin na sauya sheka ne saboda neman tsira daga binciken hukumomi kamar su hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya ce ga 'yan PDP, ADC fiye da 60,000 da suka koma APC a Jigawa

Okorie ya ce tsoron EFCC ya jawo sauya sheka
Hoton jami'an EFCC a bakin aiki Hoto:Economic and Finacial Crimes Commission
Source: Getty Images

A hira da ya yi da jaridar Vanguard, Cif Okorie ya bayyana cewa suna ganin za su samu kariya daga kamun hukumar EFCC bayan karewar wa’adinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okorie ya caccaki wasu shugabannin Najeriya

Cif Chekwas Okorie ya zargi shugabannin da ke sauya sheka da amfani da mukamansu ta hanyar da ba ta dace ba.

Ya kara da zargin cewa sun ci amanar ofishinsu kuma suna ƙoƙarin guje wa kunya da ladabtarwa daga hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa.

Okorie ya caccaki wasu daga cikin masu sauya sheka
Jagora a APGA, Cif Chekwas Okorie Hoto: APGA
Source: UGC
“Yawancin gwamnoni da ke yin gaggawar shiga APC daga jam’iyyun adawa suna yi ne saboda suna tunanin za su samu kariya daga EFCC bayan wa’adinsu ya ƙare."
"Dama daga cikinsu, wasu sun ci amanar kujerunsu tare da aikata laifuffuka ta amfani da damar da suka samu. Yanzu haka suna amfana da kariyar da Sashe na 308 na Kundin Tsarin Mulki ya tanada.”

Okorie ya kore yiwuwar zama karkashin jam'iyya daya

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 na shirin shiga APC, Gwamna Bala ya yi magana kan masu ficewa daga PDP

A cewar Okorie, ra’ayin Najeriya ta zama ƙasa mai jam’iyyar siyasa ɗaya abu ne da ba zai yiwu ba saboda bambance-bambance da ke tsakanin al’ummarta.

Ya ce:

“Najeriya ƙasa ce mai yawan kabilu da al’adu. Ba za ta iya zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba. Ba China ba ce, ba kuma Rasha ba ce da irin tsarin dimokradiyyarsu.”

Ya soki tanadin kundin tsarin mulki da ke cewa Najeriya ba za ta rabu ba kuma ba za a iya tattauna kanta ba, yana mai cewa hakan ƙarya ce da aka dade ana fada wa kai.

Ya ce:

“Mun kusa rabuwa har na tsawon watanni 30 a lokacin yakin basasa. Har yanzu Najeriya ba ta zama ƙasa guda ba, maimakon haka ta fi zama abin da Awolowo ya kira da shiyyoyi."

Okorie ya kuma zargi gwamnatocin APC — daga Buhari zuwa Tinubu — da kawo baraka a tsakanin ƙabilu da ƙara rura wutar kabilanci.

EFCC ta magantu kan binciken Okowa

A baya, mun wallafa cewa Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa ba a wanke tsohon 'dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa, Ifeanyi Okowa ba daga zargin da ke kan shi.

Kara karanta wannan

Mai Wushirya: Bayan tsawon lokaci yana bidiyon fitsara da wadarsa, kotu ta dauki mataki

A cikin wata hira da ya yi bayan Okowa ya sauya sheka zuwa APC, shugaban EFCC ya roƙi ‘yan Najeriya da su ƙara haƙuri da tsarin gudanar da shari’o’i, musamman na manyan mutane.

Shugaban ya bayyana takaicin yadda aka samu wasu na kokarin jefa shakku a zukatan jama'a game da aikin hukumar na binciken manyan mutane da ake zargi da aikata laifi a kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng