Jagora a APC Ya Fadi Makomar Tinubu, Dikko Radda a Zaben 2027

Jagora a APC Ya Fadi Makomar Tinubu, Dikko Radda a Zaben 2027

  • Jagora a jam'iyyar APC, Abdul’aziz Maituraka ya bayyana abin da zai faru da Bola Ahmed Tinubu da Dikko Umaru Radda idan su ka sake takara
  • Ya ce dukkanin jagororin sun yi abin a zo a yaba, saboda da haka 'yan Najeriya za su mayar da su ofis a babban zaben da zai gudana a 2027
  • Alhaji Abdul’aziz Maituraka ya roki mata da su ci gaba da rike alkawarin APC yayin da a ke shirin tunkarar zaben da ya fara daukar hankali

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Abdul’Aziz Maituraka, ya bayyana dalilinsa na samun tabbacin nasarar jam’iyyar a babban zaben 2027 mai zuwa.

Maituraka, Mai Taimakawa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ne kuma Mai ba Gwamna Dikko Radda shawara na musamman.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya ce ga 'yan PDP, ADC fiye da 60,000 da suka koma APC a Jigawa

Jagora a APC ya na da yakinin Tinubu da Radda za su ci zabe
Shugaba Bola Tinubu, Dikko Umaru Radda Hoto: Hoto: @DOlusegun, @dikko_radda
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ya bayyana haka ne yayin wani taro da ya da kungiyoyin matasa, zawarawa, tsofaffin kansiloli da magoya bayan APC a jihar Katsina a ranar Lahadi.

Maituraka: 'APC za ta ci zaben 2027'

A cewarsa, shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaben shugaban kasa, yayin da Gwamna Dikko Radda zai sake komawa kujerarsa a jihar Katsina.

Hadimin Gwamnan ya yaba da rawar da mata suka taka a zaben 2023, yana mai bayyana su a matsayin masu cika alkawari.

Ya kara da mika kokon barar APC ga matan, tare da bukatar su ci gaba da irin wannan kokari a zaben 2027 mai zuwa.

Jagoran APC ya roki mata su sake zaben Tinubu
Hoton Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Maituraka ya ce:

“Mata sun taka gagarumar rawa a nasarar APC a 2023. Muna rokon su da su ci gaba da jajircewa kamar yadda suka yi a baya. Ayyukan da APC ke yi a Najeriya sun bayyana karara ga kowa.”

Kara karanta wannan

Daga faduwa zaben cike gurbi, dan takarar jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa APC

Jigo a jam'iyyar APC ya fara kamfen

Maituraka ya gargadi al’umma da su guji yada jita-jita da ya ce jam’iyyun adawa ke yi don karkatar da hankali daga ayyukan da ake yi.

Ya ce:

“Kada ku bari jam’iyyun adawa su ruɗe ku. APC ce jam’iyyar da ya kamata a marawa baya a Katsina. Gwamna Radda ya fi cancanta kuma ya fi kowa dacewa da zaman wannan kujera."

Ya jaddada irin kokarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi wajen dakile matsalar tsaro da kuma bayar da dama ga mata su shiga harkokin kasuwanci.

A ƙarshe, Maituraka ya bukaci hadin kai daga dukkannin kungiyoyi, matasa da mata domin tabbatar da nasarar jam’iyyar kamar yadda aka yi a 2023.

'Yan adawa sun koma APC

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi yan PDP da ADC sama da 64,000 waɗanda suka yanke shawarar barin jam’iyyunsu suka koma APC mai mulki.

A yayin taron karɓar waɗannan sababbin 'yan jam'iyya, Tinubu ya bayyana cewa daga yanzu za a ɗauke su daidai da tsofaffin 'ya'yan APC ba tare da an nuna masu wariya ba.

Kara karanta wannan

Gwamna na shirin komawa APC, tsohon jagora a Majalisar Dattawa ya fice daga PDP

Tinubu, wanda gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya wakilta, ya ce gwamnati za ta kammala aikin hanyar Kano zuwa Maiduguri domin sauƙaƙa sufuri da bunkasa tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng