Murabus din Ministan Tinubu Ya Bude Wa Gwamna Kofa, An Nemi Ya Fice daga PDP zuwa APC
- Jiga-jigan APC a jihar Enugu sun ci gaba da zawarcin Gwamna Peter Mbah bayan Uche Nnaji ya yi murabus daga matsayin Minista
- Jam'iyyar APC ta reshen Enugu na fama da rikicin cikin gida tun da dadewa, lamarin da wasu ke ganin lokaci ya yi da za a warware matsalar
- Tsohon kakakin kwamitin kamfen Tinubu/Shettima, Denge Onoh ya roki Gwamna Mbah ya watsar da PDP, ya karbi jagorancin APC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Bayan murabus ɗin da Ministan Kimiyya da Fasaha, Chief Uche Nnaji ya yi, an kara bude wa Gwaman Peter Mbah na jihar Enugu kofar shiga APC.
Tsohon kakakin kwamitin kamfen Tinubu/Shettima a Kudu maso Gabas, Denge Josef Onoh, ya yi kira ga Gwamna Peter Mbah, ya baro PDP zuwa APC.

Source: Facebook
Mista Onoh ya gode wa tsohon minista saboda jajircewarsa da gudunmawar da ya bayar ga APC a lokacin da ya shafe a cikin gwamnatin Tinubu, in ji The Nation.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC a jihar Enugu ya kuma ba da tabbacin cewa Nnaji zai ci gaba da taka rawar gani wajen kawo ci gaba ga al’umma.
An bukaci Gwamna Mbah ya dawo APC
Da yake magana kan Gwamna Mbah, Onoh ya bayyana cewa abin da jihar Enugu ke bukata yanzu shi ne haɗin kai da jagoranci mai hangen nesa a cikin jam’iyyar APC.
Ya bayyana damuwa kan yadda APC ta jihar Enugu ta sha fama da rikice-rikicen cikin gida da rashin daidaito tun 2015, wanda hakan ya hana jam’iyyar samun nasarori a zabe.
“Ina kira ga mai girma Gwamna Peter Mbah da ya shigo cikinmu ya karbi jagorancin APC a Jihar Enugu, domin kawo haɗin kai da zaman lafiya cikin jam’iyyar.
"Ina roƙonsa da ya mayar da hankali kan daidaito da sulhu tsakanin ‘yan APC daga shugabannin jiha zuwa masu kasa, domin kafa jam’iyya ɗaya mai ƙarfi,” in ji Onoh.
Jigon APC ya hango nasarar Tinubu a 2027
Ya kara da cewa, idan aka bai wa Gwamna Mbah damar jagoranci tare da haɗa dukkan masu ruwa da tsaki, APC za ta iya dawo da martabarta a matsayin jam’iyyar da za ta jagoranci farfaɗowar Enugu.
A ruwayar Daily Trust, Onoh ya ce:
"Ina tabbatar maku cewa idan muka dunkule wuri daya, ni da abokaina da sauran 'yan jam'iyya, za mu hadu mu marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin lashe kuri'un Enugu a zaben 2027."

Source: Twitter
Mista Onoh ya ce, idan Gwamna Mbah ya karbi jagorancin APC, tare da goyon bayan tsofaffin gwamnoni kamar Sanata Chimaroke Nnamani, Ifeanyi Ugwuanyi, da Sanata Ken Nnamani, jihar Enugu za ta kere tsara.
Sanatan Enugu ya sauya sheka zuwa APC
A wani labarin, kun ji cewa sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Kelvin Chukwu ya sauya sheka daga LP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar sauya shekar Sanata Kelvin Chukwu ga sauran abokan aikinsa a ranar Laraba.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Bamidele ya ce APC na kara karbuwa a fadin kasa ne saboda salon mulkinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

