Saura kiris: Tsohon Hadimin Buhari Ya Fadi Gwamnonin Arewa da Za Su Koma APC
- Tsohon hadimin marigayi Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana gwamnonin Arewa da za su koma APC nan bada jimawa ba
- Bashir Ahmad wanda ya nemi tikitin majalisa a 2023 ya bayyana cewa gwamnonin sun fito ne daga Arewa masu Gabas da Arewa maso Yamma
- Tsohon hadimin na Buhari ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Talata, 7 ga watan Oktoban 2025
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon hadimin marigayi Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya ambato wasu gwamnonin jam'iyyun adawa da za su koma jam'iyyar APC mai mulki.
Bashir Ahmad ya bayyana cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas na jam'iyyar PDP, tare da wani gwamna daga yankin Arewa maso Yamma za su koma APC.

Source: Twitter
Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Talata, 7 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu gwamnonin adawa sun koma APC
A halin yanzu, daga cikin gwamnonin yankin Arewa maso Yamma, gwamnonin Zamfara da Kano ne kawai ke cikin jam’iyyun adawa, Dauda Lawal (PDP) da Abba Kabir Yusuf (NNPP).
Akalla gwamnonin jihohi biyu ne suka bar jam'iyyar PDP zuwa APC, tun bayan hawan Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Gwamnonin da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC su ne Sheriff Oborevwori na Delta da Umo Eno na Akwa Ibom.
"Nan da wasu 'yan kwanaki masu zuwa, gwamnan jihar Taraba da wani gwamna daga Arewa maso Yamma, za su shigo babbar jam'iyyarmu ta APC a hukumance."
- Bashir Ahmad
'Yan Najeriya sun yi martani
Kalaman na Bashir Ahmad sun jawo martani da ra’ayoyi daban-daban daga wajen ‘yan Najeriya.
Ga wasu daga ciki:
Zola Martins:
“Shin hakan zai dakatar da kashe-kashen Kiristoci da Musulmai a Arewacin Najeriya? Shin jam’iyyarku ta taɓa yin wani abin kirki wajen rage wannan bala’i? Idan har marigayi Buhari bai iya kawo jiharsa ba ga jam’iyyarku, to meye amfanin wannan sauya shekar?”
Ebuka Emma:
"Dukkan gwamnonin Najeriya ma za su iya komawa APC idan suna so, amma abin da muke bukata shi ne gyaran tsarin zaɓe. 36 + 1 ba zai taɓa rinjayar sama da mutane miliyan 200 ba.”
Solomon Adeyemi:
“Ana cewa ma gwamnan Enugu yana dab da sauya sheƙa. To me ke haifar da wannan yawan sauya shekar? Yaya tasirin hakan ga dimokuraɗiyyar mu? Lallai abin damuwa ne.”
Adnan Abdullahi Adam:
"Ba tare da maguɗi ko amfani da ƙarfin iko ba, ban ga yadda Tinubu zai iya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba. Babu wani gwamna da zai iya ba da mulki face da izininsa Allah.”
Usama Jagaba:
"To yaya hakan zai taimaka wa talakawan da ke kokarin samun abinci ga iyalansu ƙarƙashin manufofin tattalin arziƙin APC masu cutar da jama’a?"

Source: Twitter
Ba ruwan talaka da sauya sheka
Abubakar Bello Yugudu ya shaidawa Legit Hausa cewa ba damuwar talaka ba ce sauya shekar gwamnoni.

Kara karanta wannan
An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu
"Gwamnoni za su iya su yi ta sauya shekarsu ba damuwar talaka ba ne hakan. Abin da muka sani kawai shi ne duk wanda ya yi da kyau zai ga da kyau a zaben gaba."
"Wasu daga cikinsu na ganin komawa APC ne zai sanya su sake darewa kan kujerunsu, ba su san cewa kan mage ya waye ba."
- Abubakar Bello Yuguda
An bukaci gwamnan Taraba ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kungiyar matasan jihar Taraba, ta bukaci Gwamna Agbu Kefas ya hada kai da Shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar ta koka kan yadda aka bar wasu muhimman ayyuka na gwamnatin tarayya suka lalace a jihar.
Ta nuna cewa idan har Taraba ta zama jihar APC, hakan zai kawo ayyukan ci gaba, hanyoyi, da damar ayyukan yi ga matasa a cikin jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

