Sallama da Murabus: Jerin Ministoci 9 da Aka Rasa a Gwamnatin Bola Tinubu
Tun bayan darewa karagar mulki a 2023, Shugaba Bola Tinubu ya sallami ministoci biyar yayin da wasu suka yi murabus a karan kansu saboda dalilai daban daban.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A jiya Talata 7 ga watan Oktobar 2025, an samu karin minista daya da ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu tun kafin a dakatar da shi.
Uche Nnaji ya ajiye aikin nasa ne bayan an bankado cewa ya gabatar da takardun bogi na digiri da na gama NYSC ga majalisa yayin tantance shi.

Source: Facebook
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da haka a shafin X inda ya ce Bola Tinubu ya amince da murabus din Uche Nnaji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministocin da aka kora ko suka yi murabus
Gwamnatin Bola Tinubu ta rasa akalla ministoci guda tara tun bayan nadinsu a watan Agustan shekarar 2023.
Daga cikinsu akwai wadanda shugaban da kansa ya sallama yayin da wasu suka yi murabus saboda wasu dalilai ko zarge-zarge.
1. Dr. Betta Edu - Cross River
A ranar 8 ga watan Janairun 2024, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Dakta Betta Edu daga matsayin ministar harkokin jin kai da yaƙi da talauci kan badaƙalar kuɗi.
Shugaban ƙasar ya kuma umarci hukumar EFCC ta gudanar da bincike kan zargin badakalar wasu makudan kudi a ma'aikatarta ta jin kai da walwalar al'umma har N585m.
Wata wasiƙa da ta bayyana mai ɗauke da sa hannun Dr. Edu da adireshin Akanta Janar ta ƙasa ta nuna cewa dakatacciyar ministar ta ba da umarnin tura wasu kudi a asusun kai da kai na Bridget Mojisola Oniyelu.
2. Simon Lalong - Plateau
Simon Lalong ya sauka daga kujerarsa ta Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, ya zabi ya zama Sanata mai wakiltar Plateau ta Kudu.
Tsohon gwamnan ya tafi majalisar dattawa ne bayan nasarar APC a kotun karar zabe inda ya zabi zama Sanata madadin na zama a majalisar zartarwa.
Legit Hausa ta tabbatar da cewa Simon Lalong ya ajiye aikinsa ne a watan Disambar 2023 bayan shafe watanni hudu kan kujerar minista.
3. Uju-Kennedy Ohanenye - Anambra
Tsohuwar ministar mata a Najeriya ta rasa kujerarta a ranar 24 ga watan Oktobar 2024 bayan shafe shekara a mulkin Bola Tinubu.
Ohanenye ta sha jawo maganganu a gwamnatin wanda ya hada da jawo fada a wurin taro da ma'aikatar ta shirya a birnin Abuja.
Har ila yau, ministar ta yi barazanar maka Majalisar Dinkin Duniya a kotu kan kudin da suke kashewa da kuma barazanar hana daukar nauyin auren yan mata a Niger.
4. Farfesa Tahir Mamman - Adamawa
Farfesa Tahir Mamman wanda ya fito daga jihar Adamawa a Arewacin Najeriya ya rasa kujerarsa rana daya da Uju-Kennedy.
Da aka yi garambawul a majalisar FEC, Ohanenye da Mamman da wasu sun rusa kujerunsu.
Kafin rasa mukaminsa, Tahir Mamman ya jagoranci ma'aikatar ilimi wanda wasu ke ganin an sauya shi ne daga mukamin saboda rashin katabus.
5. Abdullahi Tijjani Gwarzo - Kano
Tsohon ministan daga jihar Kano ya rasa kujerarsa bayan Bola Tinubu ya sallami ministoci guda biyar a rana guda.
Gwarzo ya jagoranci ma'aikatar gidaje da raya birane a matsayin karamin minista kafin sallamarsa a karshen shekarar 2024.
Daga bisani, Bola Tinubu ya maye gurbinsa da Abdullahi Ata daga jihar wanda har yanzu ke rike da mukamin.
6. Lola Ade-John - Lagos
Lola Ade-John wacce tsohuwar ma'aikaciyar banki ce kuma masaniya a bangaren fasaha da bayanai na zamani ce na daga cikin wadanda suka rike mukamin minista a 2023.
Ade-John ta samu mukamin ministan yawon bude ido a watan Agustan 2023 inda ta shafe shekara guda kafin Bola Tinubu ya kore ta a watan Oktobar 2024.
7. Jamila Bio Ibrahim - Kwara
Matashiyar da ta fito daga jihar Kwara ta kasance yar gwagwarmaya wacce ta rike shugabancin kungiyar ci gaban matasa mata (PYWF).
Jamila ta rike mukamin minista a ma'aikatar matasa na tsawon shekara daya kafin rasa mukamin tare da wasu ministoci biyar.
Daga bisani, an maye gurbinta da karamin minista a ma'aikatar daga jihar Ogun, Ayodele Olawande wanda har yanzu ke rike mukamin.
8. Uche Nnaji - Enugu
A jiya Talata 7 ga watan Oktobar 2025, Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Uche Nnaji ya yi murabus daga mukaminsa.
A makon da ya gabata ne aka fitar da rahoto da ke nuna cewa Nnaji na amfani da takardun kammala karatu na bogi daga jami'ar Nsukka da ke jihar Enugu.
Daga bisani, jami'ar ta tabbatar da labarin, inda ta ce Uche Geoffrey Nnaji ba shi daga cikin wadanda su ka kammala karatu daga jami'ar.
9. Nentawe Yilwatda
Nentawe Yilwatda yana cikin ministocin da suka bar kujerarsu daga lokacin da Bola Tinubu ya karbi mulkin Najeriya a a 2023 zuwa yanzu.
Yilwatda ya yi murabus daga matsayin minista ne sakamakon nada shi sabon shugaban APC da aka yi bayan tafiyar Abdullahi Ganduje.
Farfesan ya canji Simon Lalong ne wanda ya bar FEC domin zama Sanatan Filato sakamakon nasarar APC kan PDP a shari'ar zaben 2023.

Kara karanta wannan
An bazo wa Minista wuta, Hadimin Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya tsige shi nan take
Shugaban hukumar INEC ya sauka daga mukaminsa
A wani labarin Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC bayan karewar wa'adinsa na biyu.
Farfesa Yakubu ya mika ragamar shugabancin hukumar ga May Agbamuche, wacce za ta rike INEC kafin nadin sabon shugaba.
Tun a shekarar 2015, marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada Mahmood Yakubu a matsayin shugaban INEC na kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



