‘Da Allah Na Dogara’: Abba kan Barazanar da Ake Yi Masa game da Zaben 2027
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi magana kan wasu kalamai da ake yadawa game da zaben shekarar 2027 da ke tafe
- Abba Kabir Yusuf ya ce shekarar 2027 ta Allah ce, kuma ba zai bari barazana ta siyasa ta hana shi ci gaba da ayyukan alheri ba a Kano
- Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin rabon tallafin ₦150,000 ga marasa karfi, inda ya zargi wasu da yada jita-jita kan gwamnatinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi maganganu game da barazanar da ake yi masa kan zaben shekarar 2027.
Gwamna Abba ya fusata da irin abubuwan da ake fada wadanda suka yi kama da yi masa barazanar kin zabensa a 2027 da ke tafe.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Legit Hausa ta gano a shafin X wanda @jibreelKhalil ya wallafa a jiya Talata 7 ga watan Oktoban 2027 da muke ciki.
Jibreel Khalil ya saba yin magana game da harkokin mulki da kuma maganganun da ake yi game da sabanin malaman addinin musulunci.
Abubuwan da ke faruwa da suke jawo maganganu
Wannan furuci na gwamnan ya zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa gwamnatinsa na iya sakin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Malamin ya shafe sama da shekaru hudu a gidan yari bayan hukuncin da aka yanke masa kan zargin taba kimar Manzon Allah SAW.
Haka kuma, ana zargin gwamnati da kokarin amfani da karfin mulki wajen hukunta Malam Lawan Triump, abin da wasu ke ganin zai iya jefa shi cikin matasala a 2027.
Sakamakon haka, wasu malamai da masu fada a ji sun fara bayyana cewa za su fito da katin zabe domin kauracewa gwamnatin jihar a zaben 2027.

Source: Facebook
Kalaman Abba Kabir bayan masa barazana a 2027
A cikin bidiyon, Abba Kabir ya bayyana cewa shekarar 2027 ta Allah ce, don haka babu wanda zai iya tsoratar da shi ko ya razana gwamnatinsa.
Gwamnan ya fadi hakan ne yayin wani taron rabon tallafin N150,000 ga marasa karfi a fadin jihar, inda ya ce wasu na ta yada jita-jita da kalamai marasa tushe game da gwamnati.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce:
“Shekarar 2027 ta Allah ce, ba ta kowa ba, Don haka, mu ba mu jin tsoron kowa, domin ba za a iya tsoratar da mu ba.”
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali kan inganta rayuwar talakawa, ba tare da tsoron masu suka ko barazana ba.
Kano: Malami ya fadi shirinsu kan zaben 2027
Mun ba ku labarin cewa zargin da ake yi wa Sheikh Abubakar Lawan Triumph a Kano ya fara sauya salo, yayin da aka fara yi wa gwamnatin Kano barazana game da zaben 2027.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ministan Tinubu zai fito bainar jama'a kan zargin amfani da digirin bogi
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana cewa suna da shiri na musamman kan zaben 2027 domin su tabbatar da wanda zai tsaya tsayin daka wajen kare addini.
Malamin ya shawarci Ahlus Sunnah da su yanki katin zabe domin tabbatar da muradinsu, yana mai cewa su ne suka fi yawa a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

