PDP Ta Yi Rashi, Tsohon Ɗan Majalisar Dattawa Ya Yi Murabus daga Jam'iyya
- PDP ta rasa babban jigon bayan tsohon sanatan Edo ta Kudu, Ehigie Uzamera, ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar
- A cikin wasikar da ya aika wa shugaban jam’iyyar a mazabarsa Uzamera ya ce ficewarsa ba ta da nasaba da rikici ko barazana
- Yayin da ya godewa PDP bisa damarmakin da ta ba shi, ana zargin tsohon sanatan zai koma jam'iyyar hadaka ta ADC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta rasa babban jigonta a jihar Edo, yayin da tsohon sanata, Ehigie Uzamera ya yi murabus.
Legit Hausa ta fahimci cewa, Ehigie Uzamera da shi ne tsohon sanata, wanda ke wakiltar mazabar Edo ta Kudu a majalisar dattawa.

Source: Twitter
Edo: Tsohon sanata ya fice daga PDP
Jaridar Daily Trust da ta fitar da rahoton ta bayyana cewa tsohon dan majalisar dattawan bai kai ga faɗin sabuwar jam'iyyar da zai shiga ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma dai, rahoton ya nuna cewa akwai alamu na Ehigie Uzamera zai koma jam'iyyar haɗaka ta ADC, don hadewa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Ehigie Uzamera ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a cikin wasikar da ya aikewa shugaban jam'iyyar na Ward 12, karamar hukumar Ovia ta Arewa, Mr. Osaigbovo Godspower.
Tsohon 'dan siyasar ya jaddada cewa bai fice daga jam'iyyar PDP saboda wata barazana, matsala ko bacin rai ba.
Ya bayyana cewa, ya yanke shawarar hakura da jam'iyyar ne saboda neman wata jam'iyyar da za ta ba shi damar ci gaba da hidimtawa jama'arsa.
Dalilin tsohon sanata na barin jam'iyyar PDP
Jaridar PM News ta rahoto wani bangare na wasikar Ehigie Uzamera ta na cewa:
"Ita siyasa, ana yin ta ne domin hidimtawa jama'a, tamkar wata mota ce da direban ke tuka mutane zuwa inda suke so su je cikin sauki.

Kara karanta wannan
An taso gwamna a Arewa a gaba ya koma APC, Tinubu zai iya karasa aikin da Buhari ya watsar
"Ta hanyar siyasa ne shugabanni ke nuna kwazonsu wajen kawo abubuwan ci gaba da gina rayuwa ga al'ummarsu, ci gaban da kowa zai shaida.
"To sai dai kuma, ana ci gaba da samun sauye sauye a yanayin siyasar Najeriya, yadda siyasar take a jiya, ba haka take a yau ba.
"Saboda wannan ne, ya sa nake ganin ya dace na sauya jam'iyya, in nemi wata jam'iyyar da za ta yi dai dai da bukatuna da burina na yi wa jama'a ta hidima."

Source: Twitter
Tsohon sanata ya godewa jam'iyyar PDP
Tsohon sanatan ya ce yana bin tafarkin akidarsa ta "Aiguiyekampe," watau a yi siyasa ba da gaba ba, kuma siyasa ta ƴanci.
"Wannan mataki da na dauka, yana cike da dogon nazari, da kuma burina na ci gaba da al'ummata hidima, ba wai don wata ƙiyayya ba."
- Sanata Ehigie Uzamera.
A karshe, tsohon sanatan ya nuna matukar godiyarsa ga jam'iyyar PDP bisa damarmakin da ta ba shi, da kuma nasarorin da ya samu a cikinta.
Tsohon sanata ya fice daga PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Kebbi ta samu nakasu bayan daga cikin manyan 'ya'yanta ya yi murabus.
Sanata Isa Galaudu wanda ya taba wakiltar Kebbi ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya, ya sanar da ficewarsa daga PDP.
Tsohon dan takarar gwamnan na PDP a zaben 2019, ya ce daya daga cikin dalilinsa na fice daga jam'iyyar shi ne yadda abubuwa suka tabarbare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

