'Lokaci na ne,' Ministan Tinubu Zai Kara Gaba, Ya Ayyana Neman Takarar Gwamna
- Ministan makamashin Najeriya, Bayo Adelabu, ya fito fili ya jaddada kudirinsa na shiga tseren takarar gwamnan Oyo a 2027
- Mista Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ya bi matakai da dama na neman gwamnan tun 2019 kuma lokaci ya yi da zai mulki Oyo
- Ya yi amfani da kalmar “Emi lokan” wadda ke nufin “Lokaci na ne” da Bola Tinubu ya yi amfani da ita a lokacin yakin zabensa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Ministan makamashi na Najeriya, Bayo Adelabu, ya bayyana niyyarsa ta sake neman kujerar gwamnan Oyo a zaben 2027.
Yayin wani taron jama’a, Adelabu ya ce ya dade yana fafutukar neman wannan kujera, kuma ya yi imani cewa lokaci ya yi da zai jagoranci jihar.

Source: Twitter
Ministan Tinubu ya nuna sha'awar takarar gwamna
Jaridar Vanguard ta rahoto ministan makamashin yana cewa:

Kara karanta wannan
'Za a maimata June 12': Malami a Kaduna ya yi hasashe mai ban tsoro kan zaben 2027
“Gaskiya ne, na jima a wannan tafiya. Ba a samun mukami nan take bayan shiga siyasa. Na bi matakai kuma na biya kudin shiga. Na tsaya takara da Seyi Makinde a 2019, sannan a 2023, lokacin yana mulki.
“A 2027, Allah ya nuna min cewa lokaci na ne. Emi lokan o, Adelabu lo kan! Lokaci na ne kuma abin da ya zama nawa ya zama na kowa ne.
" Akwai aiki mai yawa a gaban mu, dole ne a samu hadin kan kowa a cikin jam’iyya domin mutum daya ba zai iya yin komai shi kadai ba.”
Kalmar “Emi lokan”, wadda ke nufin “Lokaci na ne”, ta shahara a lokacin yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu a 2023, kuma yanzu Adelabu ya yi amfani da ita don bayyana kudirinsa.
Tarihin siyasar ministan makamashi, Adelabu
Adelabu ya bar mukaminsa na mataimakin gwamnan ayyuka a Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar 15 ga Yuli, 2018, domin tsayawa takarar gwamnan Oyo a karkashin jam’iyyar APC.
Kafar watsa labarai ta TCV News ta rahoto cewa ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar amma ya sha kaye a hannun Seyi Makinde na PDP a babban zaben 2019.
A 2022, bayan ya sha kaye a zaben fitar da gwani na APC hannun tsohon sanata Teslim Folarin, Adelabu ya fice daga jam’iyyar zuwa AP, inda ya sake tsayawa takarar gwamna bayan janyewar Ayodele Oyajide.
Sai dai kuma, a karo na biyu, ya sake shan kaye a hannun Makinde, lokacin da aka kada kuri'a a zaben 2023.

Source: Twitter
Komawarsa APC da ba shi minista
A ranar 27 ga Yuli, 2023, shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya sunan Adelabu a jerin ministoci 28, kuma majalisa ta tabbatar da shi a matsayin ministan makamashi a 16 ga Agusta, 2023.
Bayan nadin nasa, Adelabu ya koma jam’iyyar APC a shekarar 2023, inda ya bayyana cewa ya koma ne ba don son kai ba, sai don nuna goyon baya ga Tinubu.
“Na dawo ba saboda nufin zama gwamna a 2027 ba, ko don in kwace jam’iyya, amma saboda wannan jam’iyya ce da ta kawo Shugaba Bola Tinubu mulki, kuma muna bukatar mu goyi bayansa domin cika alkawuransa."
Fasto zai tsaya takarar shugaban Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, malamin coci, Odumeje ‘Indaboski’ ya ayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2027.
A yayin wata huduba mai zafi da ya gabatar ga mabiyansa, Fasto Odumeje ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugaba mai jini a jika.
Bidiyon da ke nuna lokacin da Fasto Odumeje ya nuna sha'awar tsayawa takara ya yadu sosai, ya haifar da cece-kuce a tsakanin 'yan soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng

