'Yan Siyasan da ADC Za Ta Bukaci Su Yi Murabus, Su Shigo cikin Jam'iyya Gaba Daya
- Jam’iyyar gamayyar hadakar adawa ta ADC ta umarci manyan abokan kawancenta da su kawo karshen raba kafa da su ka yi
- Sakataren yada labaran jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ne ya sanar da manyan da su ka jagoranci kafa hadakar adawa
- Daga cikin waɗanda ake nema su rungumi ADC hannu bibiyu akwai tsofaffin yan takarar Shugaban Kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Kakakin yaɗa labaran ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, an nemi jiga-jigan hadakar adawa su dawo cikinta domin kawo ƙarshen rudanin siyasa.
Haka kuma ana sa ran dawowar ta su, za ta taimaka wajen gina tsari mai ƙarfi da zai fuskanci gwamnatin APC a 2027.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa duk da jam'iyyar ba ta kayyade masu lokacin rajista na, amma ana sa ran sakon ya isa ga wadannan manyan 'yan siyasa. Sun hada da:

Kara karanta wannan
Magana ta fito, an ji dalilin da ya sa Atiku Abubakar ke jan kafa kan batun takara a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Atiku Abubakar
Atiku Abubakar, wanda ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa, shi ne ɗaya daga cikin fitattun shugabannin adawa a Najeriya.
Yana daga cikin jagororin da su ka shiga gaba, aka kuma ba ADC a matsayin dandalin da 'yan adawa za su hau, su fafata da APC.

Source: Facebook
A ranar 16 ga watan Yuli, 2025, tsohon dan takarar Shugaban Kasan ya sanar da ficewa daga jam'iyyarsa ta PDP.
Tun bayan wancan lokaci, Atiku bai kara cewa uffan a kan jam'iyyar da zai koma ba, sai dai yana gana wa da manyan yan adawa.
Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida ne a APC wanda daga baya jam'iyyar ta kore shi
Aregbesola na ɗaya daga cikin wadanda suka kafa APC, amma rashin jituwa ya sanya shi ya fice daga cikinta, kuma yana taka rawa a ADC.
Yanzu haka, tsohon gwamnan ne sakataren rikon kwarya na ADC kuma ya bayyana cewa ya karbi wannan mukami ne domin a gudu tare a tsira tare.

Source: Facebook
The Cable ta wallafa cewa a wani jawabi da ya yi a watan Yuli, da ya ke bayyana dalilin karbar mukamin, ya ce akwai bukatar 'yan siyasa su hade kansu.
Ya ce:
“Yawancin jam’iyyun siyasa da muke da su a Najeriya babu abin da suke wakilta sai tsintsiya mara igiya. Suna hade ko rabuwa ba saboda akida ko manufofi ba, sai dai kawai don neman mulki da wata fa’ida ta kai-tsaye."
2ce sama wa kasa mafita daga mulkin APC a karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
2. Malam Nasir El-Rufai
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na daga cikin wadanda su ka tsaya kai da fata wajen tabbatuwar hadakar 'yan adawa a kasar nan.

Source: Facebook
Sai dai bayan ficewarsa daga cikin APC da su ka kafa, ya sauya sheka zuwa jam'iyya mai alamar doki, wato SDP.
Duk da cewa yana halartar taruka a gidan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, har yanzu bai sanar da cewa ya koma ADC a hukumace ba.

Kara karanta wannan
Taron tsintsiya: Fadar Shugaban Kasa ta fadi kallon da Tinubu ke yi wa 'yan hadaka
3. Aminu Waziri Tambuwal
Tambuwal tsohon kakakin majalisar wakilai kuma gwamnan jihar Sokoto har sau biyu kuma yana daga cikin kusoshin hadakar adawa.
Duk da bai koma cikinta ba gaba daya, ADC ta tsaya masa wajen sukar gwamnati da EFCC bayan hukumar yaki da rashawa ta tsare shi domin amsa tambayoyi.

Source: Facebook
Ana ganin ADC bayan tsare Tambuwal:
"Wannan ba batun adalci ba ne. Wannan yunkuri ne na tilasta wa 'yan adawa su yi shiru. Ana amfani da karfin gwamnati a matsayin makami don razana ‘yan adawa kafin zaben 2027. Wannan sako ne mai tsoratarwa ga duk wani muryar da ke kokarin kalubalantar masu mulki.”
Tambuwal na daga cikin wadanda ake sa ran umarnin ADC na su daina raba kafa zai hau kansu gabanin zaben 2027.
4. Rotimi Chibuike Amaechi
Rotimi Amaechi tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas na daga cikin manyan hadakar adawa da ke sukar gwamnatin Bola Tinubu.
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa a watan Yuli na shekarar 2025, tsohon Ministan ya sanar da ficewa daga APC da ke mulki bisa zargin rashin adalci.
Amaechi ya bayyana cewa Najeriya ta shiga mummunar halin tabarbarewa gaba ɗaya, kuma tana bukatar gyara na gaggawa daga tushe.

Source: Twitter
Da yake jawabi a ranar Laraba a birnin Abuja, yayin kaddamar da kwamitin rikon kwarya na ADC, Amaechi ya zargi APC da kuma INEC da hada baki wajen cutar 'yan Najeriya.
Ya ce:
“Najeriya ta lalace kwata-kwata. Mutane ba za su iya cin abinci ba. Ba su da kudi, ba su iya siyan abinci. Komai ya lalace. Tashin farashi ya kai kololuwa.”
5. Peter Obi
Peter Obi wanda ya yi takarar Shugaban Kasa a zaben 2023 ya gabata na daga cikin jiga-jigan da su ka kafa hadakar yan adawa.
Duk da yanzu haka ana samun sabani da musayar yawu tsakaninsa magoya bayansa da tsagin Atiku Abubakar, har yanzu yana daga cikin manyan hadakar.

Source: Twitter
Har yanzu, bai sanar da ficewa daga jam'iyyar LP ba, duk da kasancewarsa a taruka daban-daban na hadakar 'yan adawa.
ADC: Obidients sun tanka Atiku
A baya, kun ji cewa magoya bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, sun yi martani mai ƙarfi ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar kan zaben 2027.
Kungiyar da ke yi wa kanta lakabi da Obidients ta nanata cewa tsohon 'dan takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar yana kalamai masu kama da wasa da hankalin jama'a.
Dr. Yunusa Tanko, wanda ya kasance tsohon mai magana da yawun yakin neman zaben Obi, ya ce akidar siyasar mai gidansa ta sauya, ba a nemi tikitin takara da Dala da shi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


