'Yan Kwankwasiyya Sun Rabu da Kwankwaso da Abba, Sun Hade da Barau a APC
- Daruruwan mambobin NNPP/Kwankwasiyya daga Bagwai da Shanono sun fice daga jam’iyyar tare da komawa APC a Abuja
- Sun jefar da jajayen huluna da suka kasance alamar Kwankwasiyya domin nuna katse alaka da tsohuwar jam’iyyarsu ta NNPP
- Sanata Barau Jibrin ya yi alkawarin cewa APC za ta ci gaba da kare muradun al’umma tare da kara ayyuka masu amfani ga jama'a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Daruruwan magoya bayan Kwankwasiyya sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa sun sauya shekar ne a wani taro da suka gudanar a gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin sauya shekar 'yan jam'iyyar NNPP
Masu sauya shekar da suka fito daga kananan hukumomin Bagwai da Shanono, sun yanke shawarin ne bayan tattaunawa da shugabanninsu.
Sun bayyana cewa sun gamsu da kokarin da APC ke yi wajen kare muradun al’umma da aiwatar da dokokin da ke amfanar jama’a.
A yayin taron, Sanata Barau ya yi maraba da sababbin mambobin, inda ya jaddada cewa APC ce jam’iyyar da ta fi karfi a nahiyar Afrika.
Sauya sheka daga Bagwai da Shanono
Kungiyar farko daga Bagwai ta samu jagorancin Alhaji Isyaku Saleh Bartawa, yayin da ta Shanono ke karkashin Abdullahi Ismail Tsaure.
Dukkaninsu sun bayyana cewa barin jam’iyyar NNPP ya zama dole saboda rashin tabbas da kuma gazawar jam’iyyar wajen cika alkawurra.
Sun kuma nuna gamsuwa da yadda APC ke tafiyar da lamuranta cikin tsarin dimokuradiyya da saukin kai ga jama’a.
'Yan NNPP sun watsar da jar hula a Kano
Wani abin da ya dauki hankali shi ne yadda masu sauya shekan suka yi watsi da jajayen huluna da suka kasance alamar Kwankwasiyya.
Wannan al’amari ya zama wani babban alamar fita daga tsohuwar jam’iyyarsu tare da tabbatar da cewa sun rungumi sabuwar tafiya.

Source: Facebook
Sanata Barau ya yi musu alkawari
Sanata Barau Jibrin, wanda ya karbi mambobin, ya yi jawabi inda ya jaddada cewa shigarsu APC zai kara karfi da ci gaba ga jam’iyyar a Kano da kasa baki daya.
Ya ce:
“Mun kuduri aniyar kawo sauyi mai amfani a rayuwar jama’a, kuma Insha Allah za mu ci gaba da tabbatar da hakan. Ku tabbata ba za mu ba ku kunya ba.”
Wasu 'yan APC sun yi Barau Jibrin fatan alheri yayin da wasu 'yan NNPP ke cewa hakan ba wani babban cigaba ba ne.
Maganar sauya shekar Kwankwaso
A wani rahoton, Legit Hausa ta hada wani rahoto kan abubuwan da za su iya faruwa idan Rabiu Musu Kwankwaso ya sauya sheka zuwa APC.
Hakan na zuwa ne yayin da aka yi rade radin cewa Rabiu Kwankwaso ya fara magana da shugaban APC na kasa.
Daga cikin abubuwan da za su iya faruwa idan ya sauya sheka akwai kulla alaka da tsohon mataimakinsa, Abdullahi Ganduje.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


