Magana Ta Fito, An Kara Samun Gwamnan PDP da Zai Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

Magana Ta Fito, An Kara Samun Gwamnan PDP da Zai Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

  • Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya gama shirin ficewa daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya
  • Majiyoyi masu karfi da ke da kusancin gwamnan sun ce an gama tattauna wa kuma kowane lokaci daga yanzu zai iya sanar da komawa APC
  • Idan hakan ta faru, Gwamna Mbah zai zama na uku da ya bar PDP zuwa APC a karkashin mulkin Bola Ahmed Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Matukar ba a samu wani sauyi ba, Gwamna Peter Mbah na Jihar Enugu zai sauya sheƙa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki.

Majiyoyi masu kusanci da gwamnan sun bayyana cewa, Mbah ya gama tattaunawa da abokan siyasarsa da shugabanni a ciki da wajen Enugu kan shirin shiga APC.

Gwamnan Enugu, Peter Mbah.
Hoton Gwamna Peter Mbah a gidan gwamnatin jihar Enugu Hoto: Peter Mbah
Source: Twitter

Rahoton da Premium Times ta tattaro ya tabbatar da cewa manyan jiga-jigai ciki har da tsofaffin gwamnoni biyu sun taka rawa wajen jawo ra'ayin Gwamna Mbah.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan tsintar gawarwakin yaran masoyin Gwamna Zulum

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ja ra'ayin Gwamna Mbah zuwa APC

Wadanda suka taimaka wajen jawo gwamnan har ya amince da shiga APC sun hada da tsoffin gwamnoni, Chimaroke Nnamani da Sullivan Chime, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani.

Wani makusancin gwamnan ya ce an kammala tattaunawa a wannan makon, kuma Gwamna Mbah da mukarrabansa za su sa ranar sauya sheka a hukumance.

Wannan mataki na Mbah zai sake zama babban koma baya ga PDP, wacce ta rike mulki a Enugu tun daga 1999, amma yanzu tana cikin rikici mai tsanani a matakin ƙasa.

Hakan dai na zuwa ne watanni bayan Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom da Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta sun bar PDP suka koma APC.

Dalilai 2 da suka sa gwamnan zai bar PDP

A cewar wani jigo na PDP, wanda ya yi ikirarin cewa Gwamna Mbah ya yi shawara da shi, gwamnan ya bayyana dalilai biyu da suka sa zai koma APC.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano za ta dauki mataki kan malamin da ake zargi da taba mutuncin Manzon Allah SAW

  • Rikicin da ya addabi PDP a matakin ƙasa, wanda ya ce barazana ce mai girma ga duk wanda yake fatan yin takara a 2027 a dandalin jam’iyyar
  • Abin da ya kira rashin adalci ga yankin Kudu maso Gabas a cikin tsarin shugabancin jam’iyyar PDP

A ranar 30 ga Yuni, gwamnan ya yi barazanar jagorantar PDP reshen Kudu maso Gabas su fice daga jam’iyyar kan rikicin kujerar sakataren PDP na kasa.

Da aka tuntubi mai magana da yawun gwamnan, Uche Anichukwu, a ranar Alhamis, ya tabbatar da cewa an yi tarukan siyasa a baya-bayan nan, amma ya ce bai da masaniya kan batun barin PDP.

Gwamna Mbah na jihar Enugu.
Hoton Gwamna Peter Mbah yana daga wa jama'a hannu a jihar Enugu Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Source: Facebook

Yaushe Gwamna Mbah zai koma APC?

Sai dai majiyoyi biyu da jaridar rahoto, duka abokan gwamnan, sun dage cewa suna da tabbaci kashi 100 cikin 100 cewa Mbah zai sauya sheƙa zuwa APC cikin ’yan makonni, ko kwanaki.

Mbah, mai shekaru 53, lauya ne, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa, wanda aka zaɓa a matsayin gwamnan Enugu a zaben 2023.

Sanatan LP ya sauya sheka zuwa APC a Enugu

A wani labarin, kun ji cewa sanata mai wakiltar jihar Enugu ta Gabas, Sanata Kelvin Chukwu ya tattara kayansa ya fice daga LP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jigawa ya bayyana matsayarsa kan tazarcen Tinubu a 2027

'Dan majalisar dattawan ya shaida wa jama'ar mazabarsa cewa ya yanke shawarar barin jam'iyyar LP ne saboda rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar.

Sanata Chukwu ya mika godiya ga jama’arsa bisa goyon bayan da suka ba shi tun lokacin da ya hau kujerar dan majalisar tarayya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262