Ana Batun Canja Sheka, Kwankwaso Ya Shiga Tattaunawa da Shugaban APC, Nentawe

Ana Batun Canja Sheka, Kwankwaso Ya Shiga Tattaunawa da Shugaban APC, Nentawe

  • Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na tattaunawa da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda
  • Rahotanni sun ce Kwankwaso ya tura wasiƙa zuwa ga Shugabancin APC, inda ya bayyana sharuɗɗan dawowarsa cikin jam’iyyar
  • Majiyoyi na cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ke bin tafarkin Kwankwaso, ya bayyana shirinsa na bin jagoransa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fara yunkuri a kan batun shiga APC.

Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka yana tattaunawa da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan yiwuwar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki.

Sanata Kwankwaso ya gana da Shugaban APC
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Kwankwaso da APC na wannan shiri ne kafin zaɓen 2027, kamar yadda majiyoyi daga jam'iyyar a Abuja su ka shaida mata.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso zai yi alaka da Ganduje idan ya koma APC da wasu abubuwa 2

APC: Kwankwaso na shiri kan sauya sheka

Majiyoyi sun bayyana cewa Kwankwaso ya aika wasiƙa zuwa ofishin APC na ƙasa a Abuja, yana sanar da niyyarsa ta shiga jam’iyyar tare da gabatar da wasu sharuɗɗa kafin dawowarsa.

Wannan wasiƙar ba ta bi matakin da aka saba ba, wato ya fara bu ta wurin jam’iyyar APC ta jihar Kano ba, sakamakon rikicin siyasa da ke tsakaninsa da shugabancin jam’iyyar na jihar.

Wata majiya daga APC ta ce:

“Mun san da wasiƙar, amma ba za mu iya magana a kai ba har sai lokaci ya yi. Amma idan yana son shigowa, babu matsala. Dama kofa a buɗe take.”

Wani babban jigo daga APC a Abuja ya bayyana cewa an shiga matakin ci gaba a tattaunawar da ke tsakanin Kwankwaso da shugabancin jam’iyyar APC.

Gwamna Abba na jiran umarnin Kwankwaso

A cewar wata majiya daga cikin gwamnati a Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna cewa yana goyon bayan matakin da jagoransa ke shirin ɗauka.

Kara karanta wannan

Da gaske Kwankwaso ya rubuta wasikar shiga APC? Madugun NNPP ya yi bayani

Majiyar ta ce:

“Gwamnanmu ba shi da wata matsala. Yana jiran amincewa daga ubangidansa ne kawai."
Rahotanni sun ce Abba na goyon bayan Kwankwaso
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto; Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Wasu daga cikin sharuɗɗan da Kwankwaso ya gabatar sun haɗa da a bar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu tikitin takarar gwamna a ƙarƙashin APC a 2027.

Haka kuma ya bukaci cewa a tabbata an ba shi mukami mai muhimmancin gaske a cikin gwamnatin APC da ke mulkin Najeriya.

Sai dai Daraktan Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa har yanzu batun wasiƙar ya fi kama da jita-jita.

“Ban da masaniya kan wani wasiƙa da Kwankwaso ya aike zuwa ga sakatariyar jam’iyya.”

Magoya bayan NNPP: Za mu bi Kwankwaso

Wasu daga cikin ƴan Kwankwasiyya, kamar Ammar Wakili Shanono ya shaida wa Legit cewa duk inda Kwankwaso ya kaɗa su, nan za su tafi.

Ya ce:

"Mu magoya bayan Kwankwaso ne, kuma ba zai ja mu ga halaka ba."

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: APC ta yi watsi da sharadin Kwankwaso na sauya sheka

A cewarsa, shi da duk wasu yan Kwankwasiyya na gaske za su bi umarnin jagoransu idan lokaci ya yi.

Ganduje ya magantu kan sauya shekar Kwankwaso

A baya, mun wallafa cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gudanar da muhimmin taro a Abuja.

A jawabin bayan taron, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ba ya zaton Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai saya sheka saboda kalaman tsohon gwamnan a kan jam'iyyar.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibril, da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun hallarci taron, wanda ake ganin shi ne irinsa na farko tun bayan da Ganduje ya yi murabus.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng