Ganduje da Jiga Jigan APC a Kano Sun Cimma Matsaya kan Batun Goyon Bayan Tinubu

Ganduje da Jiga Jigan APC a Kano Sun Cimma Matsaya kan Batun Goyon Bayan Tinubu

  • Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da wasu jiga-jigan jam'iyyar a Kano sun gudanar da taro
  • A yayin taron sun tattauna kan batun dawo da mulkin jihar Kano zuwa hannun jam'iyyar APC
  • Hakazalika sun nuna goyon bayansu ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan ayyukan da yake yi a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga jihar Kano sun gudanar da muhimmin taro a birnin tarayya Abuja.

Manyan jiga-jigan na APC sun yi taron ne domin tattauna dabarun karɓe jihar Kano daga hannun jam’iyyar NNPP.

Ganduje da jiga-jigan APC sun yi taro a Abuja
Ganduje da sauran jiga-jigan APC a wajen taron da suka yi a Abuja Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Ganduje da jiga-jigan APC sun hadu a Abuja

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa daga cikin mahalarta taron akwai mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da tsohon gwamna kuma Sanata, Kabiru Gaya, Sanata Abdulrahman Kawu Ismaila, shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abba Bichi; karamin ministan gidaje da ci gaban birane Hon. Abdullahi Yusuf Ata.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fito da bayanai kan maganar sauya shekar Kwankwaso zuwa APC

Hakazalika Sanata Basheer Lado, shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, da wasu fitattun ’yan siyasa irinsu Ibrahim Zakari, Hon. Alhassan Kabiru, Shaaban Ibrahim Sharada, Musa Ilyasu Kwankwaso, da Abdulaziz Abdulaziz sun halarci taron.

Abdullahi Ganduje ya yi bayani

Da yake magana bayan kammala taron, Ganduje ya bayyana cewa sun hadu ne domin duba halin da jam’iyyar APC ke ciki a Kano da kuma tabbatar da goyon bayansu ga shugaban kasa.

“Mun hadu ne mu jiga-jigan APC daga Kano domin mu duba halin jam’iyyarmu ke ciki da kuma tabbatarwa shugaban kasa cewa mu a Kano muna tare da shi baki ɗaya."
"Mun yaba da manufofinsa da kyakkyawan aikin da yake yi wa kasar nan, da Kano, da kuma nade-naden mukamai da ya bai wa mutanen Kano."
"Kun san abin da ya faru a zaben da ya gabata, mun kusa yin nasara, amma ba mu yi ba. Duk da haka, jam’iyyarmu ta ci gaba da kasancewa a tsaye kuma saboda manufofin shugaban kasa, mun karbi wasu manyan ’yan siyasa daga wasu jam’iyyu.”

- Abdullahi Umar Ganduje

Ya bayyana cewa a cikin waɗanda suka koma APC akwai Sanata mai ci yanzu, Ismaila Kawu Sumaila, ’yan majalisar wakilai, tsohon shugaban majalisar dokokin Kano, da kuma wasu tsofaffin ’yan majalisar jiha.

Kara karanta wannan

Barau ya hango abin da mutanen Kano za su yi wa Tinubu a 2027

Haka kuma akwai kwamishinoni da sakataren gwamnatin Jiha (SSG) daga gwamnatin NNPP da suka sauya sheka zuwa APC.

Jiga-jigan APC a Kano sun yi taro a Abuja
Sanata Barau Jibrin da Kawu Sumaila a wajen taron jam'iyyar APC Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Sanata Barau Jibrin ya yabawa Tinubu

A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin ya nuna godiya kan nade-naden mukamai da ayyukan da Shugaba Tinubu ya kawo Kano da yankin Arewa gaba ɗaya.

"Muna tare da shi gaba ɗaya domin babu abin da muka taɓa nema a wurinsa da bai yi mana ba. Mun yanke shawara a matsayin jiga-jigan jam’iyya mu koma gida mu ci gaba da karfafa mutane su goyi bayan shugaban kasa."

- Sanata Barau Jibrin

Sanata ya koma jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Kelvin Chukwu, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Sanata Kelvin Chukwu ya sauya sheka zuwa APC bayan ya tattara kayansa daga jam'iyyar LP mai adawa.

Ya bayyana cewa ya cin ma matsayar barin yanke shawarar barin LP ne saboda rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng