APC: Siyasa Ta Kara Tsami, An Shata Layi tsakanin Lamido da Wamakko a Sakkwato
- Rikicin cikin gida a jam'iyyar APC ya ƙara kamari tsakanin magoya bayan Sanata Ibrahim Lamido da tsohon gwamna Sanata Aliyu Wamakko a Sakkwato
- A bayan nan ne Sanata Aliyu Wamakko da Shugaban tsagin APC a jihar, Isa Sadiq Achida su ka bayyana shakku a kan asali da ingancin siyasar Ibrahim Lamido
- Isa Sadiq Achida, ya ce ba za a bar Sanata Ibrahim Lamido ya tsaya takara a 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar ba saboda wadannan zarge-zarge
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rikicin siyasa da ya sako APC a gaba a jihar Sokoto ya canja salo bayan magoya bayan Sanata Ibrahim Lamido sun yi martani kan kalaman Sanata Aliyu Wamakko.
Haka nan sun dura a kan da shugaban tsagin jam’iyya na jihar, Isa Sadiq Achida a kan bayyana shakku a game da ingancin siyasar Sanata Ibrahim Lamido.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa a wata sanarwa da suka fitar, magoya bayan Lamido sun ce zarge-zargen da ake masa abun dariya ne, kuma ana yinsu ne saboda tsantsar tsoro.
Rikicin APC a Sakkwato ya fara kamari
Magoya bayan sun bayyana Sanata Ibrahim Lamdio da cewa ba wai kawai ɗan siyasa ba ne, amma ɗan asalin gidan Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo ne, wanda ya kafa Daular Sakkwato.
Sanarwar ta ce:
“Tambayar asalin Lamido kamar raina jinin da ya kafa wannan jiha ne."
Sun kuma bayyana cewa hare-haren da Wamakko ke kai wa kan Lamido na da alaƙa da tsoron farin jinin matashin ɗan siyasar da kuma rashin iya sarrafa shi.
APC: Achida ya caccaki Lamido
Da aka nemi jin ta bakinsa, Isa Sadiq Achida ya dage cewa Lamido ba ɗan asalin jihar Sakkwato ba ne, yana mai cewa ba za a ba shi dama ya tsaya takara a ƙarƙashin APC a 2027 ba.

Source: Original
Ya ce:
“A matsayinsa na wanda ya soki Sanata Aliyu Wamakko da karya hadin kan jam’iyya, ba zai samu tikitin APC a Sokoto ba."
Achida ya ƙara da cewa lokaci ya wuce da baƙi ke cin moriyar arzikin mutanen Sakkwato don samun nasarar siyasa.
Sai dai magoya bayan Lamido sun ce:
“Sanata Lamido ba ya buƙatar amincewarku don ya ci gaba da buga siyasa."
Rahotonni sun bayyana cewa wannan rikicin ya raba kan sarakunan gargajiya a jihar, inda wasu ke goyon bayan bangaren Lamido yayin da wasu suka tsaya a gefen Wamakko.
Ana rikicin siyasa tsakanin Lamido da Wamakko
A baya, mun wallafa cewa ana kara samun rabuwar kai a tsakanin jiga-jigan jam’iyyar, musamman Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido a Sakkwato.
Duk da cewa APC ta samu gagarumar nasara a jihar a zaben 2023, nasarar ba ta hana barkewar rikici ba wanda ke kara tsananta a cikin jam’iyya a tsakanin manyan 'yan siyasan biyu.
Jam’iyyar APC a Sakkwato ta dare gida biyu sabida sabanin da aka samu, inda aka samu bangaren da Sanata Aliyu Wamakko ke jagoranta da kuma na Sanata Ibrahim Lamido.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


