'Za Mu Iya Shiga Hadaka,' NNPP Ta Fadi Matsayarta kan Komawar Kwankwaso APC

'Za Mu Iya Shiga Hadaka,' NNPP Ta Fadi Matsayarta kan Komawar Kwankwaso APC

  • Shugaban jam'iyyar NNPP, Ajuji Ahmed ya fayyace cewa Sanata Rabiu Kwankwaso bai nuna wata alama ta sauya sheka zuwa APC ba
  • An samu maganganu daban daban kan cewa Kwankwaso ya yanke shawarar shiga APC, bayan wasu kalamai da ya yi a Kano
  • NNPP ta yi martani cewa tana da zabubbuka uku: yin tafiya ita kaɗai, shiga kawance da jam’iyyar adawa, ko kuma su koma APC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam’iyyar NNPP, ta warware rudanin da aka samu game da cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yanke shawarar shiga APC.

Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, ba zai sauya sheka zuwa APC mai mulki ba.

NNPP ta yi karin haske kan kalaman Kwankwaso na komawa jam'iyyar APC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana jawabi a wani taron yaye dalibai da ya halarta a Kano. Hoto: @babarh_/X
Source: Twitter

Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da yake amsa tambayoyi a wata hira da aka yi da shi a shirin ‘Prime Time’ na gidan talabijin din Arise.

Kara karanta wannan

'Najeriya ba Legas ba ce,' ADC ta fadi abin da ke shirin faruwa da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman Kwankwaso kan shiga APC

A baya dai Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyarsa a buɗe take ga shiga jam’iyyar APC, amma sai dai idan aka ba da “tabbataccen alƙawari.”

Kwankwaso ya faɗi haka ne lokacin da ya karɓi Buhari Bakwana, tsohon mashawarcin siyasa na tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, tare da mambobin APC daga ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, a gidansa da ke Miller Road a Kano.

Ya tunatar da baƙin cewa shi da wasu muhimman mutane ne suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa APC a 2013, inda ya ce sun sha wahala sosai sakamakon tsangwama na siyasa a lokacin.

“Babu wanda zai gaya mini nauyin da muka ɗauka wajen kafa APC. Mu ne muka jagoranci kafuwar jam’iyyar, kuma mu ne gwamnoni bakwai na farko da suka bayyana goyon baya ga jam’iyyar. An yi amfani da ICPC, EFCC, da ‘yan sanda a kanmu a lokacin, don kawai a dakile shirye-shiryenmu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya karbi dan takarar gwamna zuwa NNPP, Kwankwasiyya na murna

- Sanata Rabiu Kwankwaso.

Karin hasken NNPP kan kalaman Kwankwaso

Jagoran na NNPP ya ce dole ne a bayyana wa jam'iyyarsa irin fa'idojin da za ta samu idan har ta shiga wata hadaka ko ta koma APC, inji rahoton Daily Trust.

Kwankwaso ya ce:

“Idan aka ce mu shiga APC, to dole ne a faɗi abin da NNPP za ta amfana da shi. Muna da ‘yan takarar gwamnoni a duk jihohi kuma muna da cikar tsari a faɗin ƙasa. Me za ku ba su idan muka shiga?"

Amma a martanin da ya yi kan jita-jitar da ke cewa Kwankwaso ya riga ya yanke shawarar shiga APC, shugaban NNPP na ƙasa, Ajuji Ahmed, ya ce:

“Ba na tunanin haka. Ba na ganin abin da ya faɗa ya nuna a cewa zai sauya sheka ko kuma yana dab da yin hakan. NNPP ta dade da daukar matsaya kan zabuka masu zuwa."

Kara karanta wannan

Sauya sheka: An fadawa Tinubu yadda Kwankwaso zai taimaka masa a 2027

NNPP ta ce tana da zabuka uku da za ta yi amfani da daya a zaben 2027
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Zabuka 3 da NNPP take da su gabanin 2027

Ajuji Ahmed ya ci gaba da cewa:

“Ɗaya daga cikin zabin da muke da shi, shi ne shiga jam'iyyar APC. Wani zaɓin shi ne mu shiga haɗaka da kowace jam’iyya da take da irin falsafa da manufofinmu.
“Zaɓi na uku kuma shi ne mu ci gaba da tafiya mu kaɗai. Don haka, waɗannan zaɓuka har yanzu suna teburinmu. Duk da haka, domin fayyace abin da Kwankwaso ya faɗa a Kano, kawai ya yi bayani ne kan ɗaya daga cikin zaɓuɓɓukan uku."

Shugaban na NNPP ya jaddada cewa, kalaman Kwankwaso ba tabbaci ne na shiga APC ba, kawai ya fadi sharadin da jam'iyya mai mulki za ta kiyaye idan tana son goyon bayansa.

'Kwankwaso zai iya komawa APC' - NNPP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban tsagin NNPP a jihar Kano, Jibril Doguwa, ya yi magana kan batun komawar Rabiu Musa Kwankwaso APC.

Kara karanta wannan

'Ba da mu ba,' NNPP ta nesanta kanta da shirin Kwankwaso na shiga APC

Jibril Doguwa ya bayyana yiwuwar cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, zai iya komawa jam’iyyar APC.

Amma shugaban na NNPP ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta iya ci gaba da rayuwa ko da ba tare da Kwankwaso ko kuma mambobin Kwankwasiyya ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com