2027: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Fara Shirin Mika Mulki, Ta Kawo Dalili

2027: PDP Ta Bukaci Tinubu Ya Fara Shirin Mika Mulki, Ta Kawo Dalili

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya na ganin lokaci ya yi da ya kamata shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fara shirin mika mulki
  • PDP ta nuna cewa yanzu 'yan Najeriya sun samu wayewar da ba za ta bari su sake damka ragamar jagorancin kasar nan a hannun Tinubu ba
  • Sai dai, APC ta yi martani inda ta nuna cewa zaben shekarar 2027, shi ne zai kawo karshen jam'iyyar PDP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya fara shirin rubuta takardun mika mulki.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa ‘yan Najeriya ba za su sabunta masa wa’adin shugabanci a shekarar 2027 ba.

PDP ta taso Shugaba Tinubu a gaba
Shugaban PDP na kasa, Umar Iliya Damagum da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialPDPNig, @DOlusegun
Source: Twitter

Sakataren tsare-tsare na PDP a jihar Adamawa, Hamza Madagali, ya bayyana hakan yayin da yake magana da jaridar The Punch a ranar Juma’a a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me PDP ta ce kan gwamnatin Tinubu?

Hamza Madagali ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da gwamnatin yanzu kuma ba za su iya jure mata ba har zuwa shekarar 2027.

Ya ce gwamnatin jam’iyyar APC ta nuna rashin hangen nesa da jagoranci na gaskiya.

Hamza Madagali ya bayyana manufofin APC a matsayin marasa tausayi ga al’umma da tattalin arziki, yana mai cewa ‘yan Najeriya sun shirya kawo karshen mulkin wannan gwamnati a 2027.

Ya kara da cewa nasarorin da aka samu a kwanan nan yayin zabukan PDP na mazabu a jihar Adamawa, alama ce ta cewa haɗin kan jam’iyyar na iya bata damar cin nasara a babban zaɓe.

"Idan ka kalli jerin mutanen da ke cikin kwamitocin babban taron kasa, za ka ga a fili cewa kwanakin APC a fadar shugaban kasa sun kusa zuwa karshe."
"‘Yan Najeriya sun waye yanzu, sun san bambanci tsakanin gaskiya da bogi. Saboda haka ba za su sake yin wasa da makomar ‘ya’yansu ba. Hanyar tsira ita ce dawo da PDP kan mulki."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya yi magana kan komawa ADC bayan rashin samun mafaka a APC

- Hamza Madagali

Jam'iyyar APC ta yi martani

Amma da yake mayar da martani kan wannan magana, wani jigo a jam’iyyar APC, Seye Oladejo, ya yi watsi da damar PDP na tunbuke Shugaba Tinubu.

PDP ta bukaci ya fara shirin bankwana da mulki
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Ya ce mutane da dama na barin PDP kullum kuma za a kawo karshenta a zaben shekarar 2027.

"Na yarda cewa ya kamata ya mika mulki, amma ya kamata ya mika mulkin ne wa kansa a matsayin shugaban kasa bayan zaɓen 2027. PDP jam’iyya ce kawai da take a takarda."
“Zaben 2027 shi ne zai zama karshen PDP. Ba jam’iyyar da za a ɗauka da muhimmanci ba ce.”

- Seye Oladejo

Jigon PDP ya magantu kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya yi magana kan zaben shekarar 2027.

Tsohon dan takarar gwamnan Ogun ya bayyana cewa zaben shekarar 2027, zai kasance ne tsakanin jam'iyyun PDP da APC.

Kara karanta wannan

'Yan fansho sun fusata, suna shirin fara zanga zanga tsirara a fadin Najeriya

Segun Sowunmi ya nuna cewa ko kadan jam'iyyar hadaka wato ADC, ba za ta kai labari ba a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng