Wike Ya Fadi Abin da Ƴan Siyasar Ribas Suka Saka a gaba bayan Dawowar Fubara
- Tsohon Gwamnan Ribas kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike ya tabbatar da cewa ya yi magana da Simi Fubara kafin dawowarsa aiki
- A ranar Alhamis ne ya kamata Fubara ya koma aiki bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta baci da ya sa a Ribas
- Wike ya ce yanzu da Fubara ya dawo, za a hada kai domin yi wa jama'a aiki ba tare da rigingimun siyasa ba kamar yadda aka samu a baya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da su ka wakan dab da dawowar Siminalayi Fubara mulkin Ribas.
Ya bayyana cewa hasali ma sai da ya tattauna da Fubara, kafin dawowarsa zuwa jihar bayan kawo karshen dokar ta-baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Source: Facebook
Wike, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nyesom Wike ya magantu kan siyasar Ribas
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Wike ya ce yanzu zaman lafiya ya dawo jihar Ribas bayan rikicin siyasa da ya dauki watanni shida.
Ya ce a ganarwar da ya yi da Fubara, sun shaida wa juna ta wayar tarho cewa za su koma Najeriya gabanin janye dokar ta bacin.
Wike ya yabawa Majalisar Dokoki ta Jihar Ribas da rawar da ta taka wajen dawo da zaman lafiya, yana mai cewa:
“Za ka iya ganin cewa muna son zaman lafiya. Muna shiri don ci gaban jihar.”
Tun a ranar 18 ga Maris, 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Ribas sakamakon rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da 'yan majalisa.
Yadda aka mulki Ribas a dokar ta baci
Bayan Shugaban kasa ya dakatar da Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da kuma ‘yan majalisar jihar na tsawon watanni shida, sai ya nada mai kula da harkokin jihar.
Bola Tinubi ya sanar da nadin Vice Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya a matsayin shugaban rikon kwarya a jihar domin ci gaba da sa ido kan harkokinta.

Source: Facebook
Wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar, inda wasu ke ganin Tinubu ya karya kundin tsarin mulki.
Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta nanata cewa matakin a matsayin dole domin kwantar da tarzoma da kare afkuwar tabarbarbarewar doka da oda.
Daga bisani, a ranar 3 ga Yuni, Gwamna Fubara ya kai wa shugaban kasa ziyara a gidansa da ke Legas, ziyarar da ta kasance karo na biyu da suka gana bayan dakatarwar.
Bayan haka ne aka samu sulhu tsakanin Fubara da Wike, inda suka fara halartar taruka tare, daga baya Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-baci, a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.
PDP ta roki gwamnan Ribas, Fubara
A wani labarin, mun wallafa cewa PDP ta roƙi Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da kada ya bar jam’iyyar, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye dokar ta-baci.
Mataimakin shugaban PDP na Legas ta Tsakiya, Hakeem Olalemi, ya bayyana cewa ya kamata Gwamna Fubara ya ci gaba da jajircewa ba tare da tsoron hidimta wa jama'arsa ba.
Hakeem Olalemi ya shawarci ‘yan siyasa a Ribas da su daina rura rikici, su rungumi zaman lafiya da hadin kai, domin inganta aikin gwamnati da al’amuran ci gaban al’umma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


