Wike Tsallake Rijiya, Ya Fadi yadda Janar na Soja Ya ba da Umarnin Harbe Shi
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce an taba ba da umarni a harbe shi a lokacin zaben 2019, amma ya tsira daga barazanar
- Ya ce tsohon hafsan sojan da ya ba da wannan umarni yanzu yana aiki a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro
- Wike ya ce a zaben 2027 zai mara wa shugaba Bola Tinubu baya, ba Atiku Abuabakar ba, musamman a jihar Rivers
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers – Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya sake waiwayar abubuwan da suka faru a lokacin zaben gwamna na 2019.
Ministan harkokin na Abujan ya bayyana cewa wani Janar din soja ya taba bayar da umarnin a harbe shi a lokacin zaben.

Source: Facebook
Wike ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi kan lamuran siyasa a tashar Channels TV ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin da aka yi a Rivers a 2019
A zaben 2019, hukumar INEC ta bayyana cewa Wike ya lashe kujerar gwamnan Rivers bayan ya samu kuri’u 886,264, yayin da abokin hamayyarsa Biokpomabo Awara ya samu kuri’u 173,857.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Awara ya lashe kananan hukumomi biyu ne kacal daga cikin 21 da aka kidaya.
Sai dai kuma, a lokacin an samu tashin hankali da tarzoma wanda ya sa hukumar INEC ta dakatar da tattara sakamakon zabe na wani lokaci.
Daga bisani, bayan taron masu ruwa da tsaki, aka amince da sake ci gaba da kidayar kuri’u a jihar Rivers.
Soja ya ce a harbe Wike a Rivers
Nyesom Wike ya ce a matsayinsa na gwamna wani babban soja ya ki ya saurare shi kuma ya bayar da umarnin a harbe shi.
Tsohon gwamnan ya ce saboda wannan abin da ya faru, bai zuwa ofishin NSA domin jami'in sojan yana aiki a nan ne a yanzu.

Kara karanta wannan
Filato: Bincike ya bankado yadda aka hallaka mutum kusan 12,000 a 'yan shekarun nan

Source: Facebook
Wike ya yi nuni da cewa siyasar Najeriya ta sha fama da irin wannan makirci, inda ake amfani da karfi da iko wajen cimma manufofin jam’iyya ko mutum.
Ya ce a lokacin, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi ya yi alkawarin ba sojan matsayin shugaban sojoji, wanda ya bayyana a matsayin babban kalubale da ya fuskanta a rayuwar siyasa.
Wike zai goyi bayan Tinubu a 2027
Dangane da makomar siyasa, Wike ya bayyana cewa a zaben shugaban kasa na 2027, ba zai mara wa Atiku Abubakar baya ba, musamman a jihar Rivers.
A cewarsa:
“Waye ne zai sa Atiku ya ci zabe a Rivers a 2027? Gwamna Fubara ba tare da su yake ba. Wa za su dogara da shi wajen samun kuɗi? Sun riga sun gaza.”
Majalisar Rivers ta ba Fubara Umarni
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokokin jihar Rivers ta fara zama bayan janye dokar ta baci da Bola Tinubu ya yi.
A zaman 'yan majalisar na farko, sun umarci gwamna Siminalayi Fubara da ya gaggauta mika sunayen kwamishinoni.
Haka zalika sun bukaci Fubara da ya mika kasafin kudin jihar su duba shi domin samun damar fara ayyukan da za a gudanar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

