2027: Za a Tarawa Tinubu Sama da Kuri'un da Kwankwaso Ya Samu a Kano a Jiha 1

2027: Za a Tarawa Tinubu Sama da Kuri'un da Kwankwaso Ya Samu a Kano a Jiha 1

  • Dattawan jam’iyyar APC a jihar Ondo sun ce za su tabbatar da shugaba Bola Tinubu ya samu ƙuri’u miliyan 1.5 a zaben 2027
  • Shugaban ƙungiyar, Sanata Nimbe Farunkanmi, ya ce za su gudanar da taruka a matakai daban-daban domin tabbatar da hakan
  • Kuri'a miliyan 1.5 da aka yi wa Tinubu alkawari a jihar ya haura adadin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya samu a Kano a 2023

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo – Dattawan jam’iyyar APC a jihar Ondo sun bayyana aniyarsu ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.

Sun yi alkawarin samar masa da akalla ƙuri’u miliyan 1.5 daga cikin masu kada ƙuri’a miliyan 1.9 da ake da su a jihar.

Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a wani taro
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa alkawarin ya fito ne daga ƙungiyar dattawan APC a jihar a wani taro da aka gudanar a babban birnin jihar, a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tinubu, Fubara sun dawo Najeriya ana shirin dawo da gwamnan Ribas kujerarsa

Shugaban ƙungiyar, Sanata Nimbe Farunkanmi, ya ce wannan yunƙuri na nufin tabbatar da haɗin kai da nasarar jam’iyyar a matakin ƙasa.

Alkawarin dattawan APC ga Bola Tinubu

Sanata Farunkanmi ya ce ƙungiyar za ta tabbatar da cewa kashi 90 cikin 100 na ƙuri’un jihar za su tafi ga Shugaba Tinubu.

Ya bayyana cewa za a gudanar da irin waɗannan tarurruka a matakin ƙananan hukumomi da unguwanni domin wayar da kan jama’a.

“Ina tabbatar muku wannan yunƙuri na tsare-tsare ne domin ci gaban mulkin Tinubu da jam’iyyar APC,”

- In ji shi.

Hanyar da za a sama wa Tinubu kuri'a

Wani daga cikin jagororin ƙungiyar, Jamiu Ekungba, ya bayyana cewa manufar taron ita ce tara jama’a tare da tabbatar da cewa sun yi rajistar yankar katin zabe.

Ya ce jam’iyyar ta riga ta fara shirin wayar da kan jama’a kan ci gaba da yin rajistar masu kada ƙuri’a da hukumar INEC ke gudanarwa.

Kara karanta wannan

'Za mu fitar da Tinubu daga Aso Rock Villa,' Aregbesola ya fadi shirin ADC a 2027

Ekungba ya kara da cewa babban kalubale shi ne rashin sha’awar mutane su fita kada ƙuri’a, amma dattawan za su yi ƙoƙarin ganin kowa ya fito ya yi zabe.

Ya ce a baya sun gwada irin wannan tsari, inda suka taimaka wa gwamnan jihar wajen samun ƙuri’u 366,000, abin da ya ce ya nuna cewa akwai yiwuwar cimma burinsu a 2027.

Kuri'un Kwankwaso a Kano a 2023

A zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi nasara a Kano da ƙuri’u 997,279, inda ya lashe kananan hukumomi 38 daga cikin 44.

Wannan adadi ya yi kasa da wanda dattawan APC a Ondo ke ganin za su samar wa Tinubu a zaben 2027.

Rabiu Kwankwaso da ya yi takarar shugaban kasa a 2023
Rabiu Kwankwaso da ya yi takarar shugaban kasa a 2023. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Maganar takarar Tinubu da Shettima

A wani rahoton, kun ji cewa tsugune bata kare ba kan maganar takarar shugaban kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima a 2027.

Tun a farkon shekarar 2025 aka fara maganganu kan sauya Kashim Shettima da wani abokin takara a zabe mai zuwa.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana wa manema labarai cewa babu maganar cewa za a sauya Shettima kwata kwata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng